Tsohon Hafsan Tsaro, Irabor Ya Tsoma Baki kan Rigimar Wike da Matashin Soja a Abuja
- Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya nuna damuwa kan halayyar da ministan Abuja, Nyesom Wike ya nuna a takaddamarsa da sojan ruwa
- Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya (CDS) ya ce kalmomin da Wike ya yi amfani da su sun yi daci, musamman ga wanda ke sanye da kakin soja
- Irabor, wanda ya jagoranci sojojin Najeriya a mulkin Buhari, ya bukaci a girmama kakin soja saboda yana wakiltar karfin ikon kasa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Babban Hafsan Tsaro na Ƙasa (CDS), Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ya yi tsokaci kan rikicin da ya faru tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike da matashin sojan ruwa.
Idan baku manta ba, Wike ya yi cacar baki har da amfani da kalamai masu zafi a rigimar da ta faru tsakaninsa da Laftanal A. M Yerima a wani fili a Abuja ranar Talata.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce yayin da yake martani, tsohon CDS ya soki yadda Wike ya yi wa matashin sojan wanda ya nanata cewa yana bin umarni daga sama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Irabor ya yi wannan bayani ne a ranar Alhamis a Abuja, a wurin taron da kungiyar Editocin Najeriya (ANEC) karo na 21.
Kalamai masu zafi da Wike ya fada
Bidiyoyi da suka yadu sun nuna yadda sojojin ruwa suka hana ministan shiga wani filin da ake takaddama a kai, lamarin da ya haifar da musayar yau zafi.
A lokacin da takaddama ta barke a tsakaninsu, Wike ya kira sojan ruwa, Laftanal AM Yerima, da kalmar “wawa”.
Da yake mayar da martani kan lamarin, tsohon CDS, Irabor ya ce babban abin dubawa shi ne kimar rigar soja da kuma rantsuwar hidimar ƙasa da ta ƙunsa.
“Kakin soja ba ruwansa da wanda ya sanya shi, wannan kaki yana wakiltar ikon kasa, ko matashi ko babba ne ya sanya kakin soja, yana wakiltar kasa ne gaba daya."
Irabor ya zargi Wike da cin mutuncin soja
Irabor ya ƙara da cewa cin mutuncin soja da irin waɗannan kalamai da Wike ya yi amfani da su tamkar cin mutuncin ikon da shugaban ƙasa ya dora a kan rundunar soji ne.
Tsohon babban hafsan tsaron ya bukaci a duba wannan abu da ya faru ta hanyar amfani da dokokin gidan soja, sannan a duba niyya da kuma aiki, in ji Vanguard.
Lucky Irabor ya ce lamarin bai tsaya iya ikon da Minista ke da shi kan filaye ko zargin matashin soja ya aikata laifi ba, sai dai kalaman Wike sun keta mutuncin kasa.

Source: Facebook
Ya yi kira ga kafafen yada labarai da su wayar da kan jama’a kan muhimmancin rantsuwar aiki da kimar kakin soja, yana mai cewa ilimin ɗabi’un ƙasa yana raguwa a Najeriya.
An bukaci Tinubu ya ja kunnen Wike
A wani labarin, kun ji cewa tsohon jagora a APC, Timi Frank ya bayyana takaici a kan rikicin Ministan Abuja, Nyesom Wike da jami'in sojan ruwa, A.M Yerima.
Ya bayyana lamarin a matsayin alama ta lalacewar tsarin shugabanci a Najeriya da kuma barazana ga dimokuraɗiyya a kasar nan.
Frank ya bukaci Tinubu ya ja kunnen Wike, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa tana mutunta doka, ladabi da kuma ƙoƙarin kare hukumomi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


