Musulunci Ya Samu Ƙaruwa, Baban Chinedu Ya ba Matashiya da Ta Musulunta Shawara

Musulunci Ya Samu Ƙaruwa, Baban Chinedu Ya ba Matashiya da Ta Musulunta Shawara

  • Wata matashiya ta karɓi Shahada a radin kanta, inda malam Adamu Ashaka da Baban Chinedu suka jagoranci addu’o’i da jan hankali
  • Baban Chinedu ya shawarce ta kan kalubalen da masu sauya addini ke fuskanta, yana mai cewa ta rungumi Musulunci saboda lahira
  • Adam Ashaka ya kara da cewa duk wanda ya musulunta ba ya rasa jarabawa, yana karfafa mata gwiwa da ta dage cikin hakuri.

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Addinin Musulunci ya samu karuwa bayan wata matashiya mai matsakancin shekaru ta karbi kalmar shahada a radin kanta.

Malam Adamu Ashaka da Yusuf Haruna da aka fi sani da Baban Chinedu su ne suka gabatar da karatu da jan hankali har aka yi wannan nasara.

Matashiya ta karbi Musulunci a Najeriya
Baban Chinedu da Adam Ashaka bayan wata ta karbi Musulunci. Hoto: Adam Ashaka.
Source: Facebook

Matashiya ta karbi addinin Musulunci a Najeriya

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Baban Chinedu wanda ya wallafa a shafin Facebook a jiya Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Bayan shekaru 9, kotu ta yanke wa mutum 4 hukuncin kisan ta hanyar rataya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon, an gano Baban Chinedu da Adam Ashaka suna tsaye yayin da me gabatarwa ya ke bayyana nasarar da aka samu.

Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025 inda matashiya ta sauya suna zuwa Husnah.

Daga bisani, Baban Chinedu ya ba ta shawarwari game da kalubalen da ke cikin Musulunci musamman ga wadanda suka Musulunta.

"Na farko akwai wanda ya tilasta ki kika shiga Musulunci? (matashiyar ta ce babu), ra'ayinki ne kuma fashimtarki ko? to Alhamdulillah.
"Allah ne ya azurta ki da addinin Musulunci don haka akwai kalubale duk da mun ji yanayin yadda gidanku suke tushe ne na Kiristanci, ba fada zaki yi da wani ba ko iyayenki.
"Ke dai yanzu ana magana ne na lahira ba duniya ba saboda duniya mutum bai wuce shekaru 150 zuwa 200 kamar yadda na fada dazu."
Matashiya ta karbi Musulunci a hannun Baban Chinedu, Ashaka
Matashi da ke da'awa na addinin Musulunci, Yusuf Haruna. Hoto: Baban Chinedu.
Source: Facebook

Shawarar da Adamu Ashaka ya ba matashiyar

Kara karanta wannan

Tsohon hafsun tsaro, Janar Chiristopher Musa ya samu sabon mukami a Amurka

Har ila yau, Adam Ashaka shi ma ya tofa albarkacin bakinsa inda ya tabbatar da cewa dola za ta fuskanci kalubale inda ya karfafa mata guiwa.

A cewarsa:

"Kamar yadda Malam Yusuf ya yi bayani, duk wanda ya musulunta yana fuskantar kalubale da yawa, shawarar da zan baki duk wani kalubale da za ku fuskanta ku yi hakuri."

Ashaka ya ba su tabbacin cewa za su ci gaba da bibiyar lamuransu ta tabbatar da cewa sun samu iliimi da sauran abubuwa na rayuwa.

Matashiyar ta tabbatar da cewa mahaifiyarta ita ce uwar zumunta inda ta bayyana cocin da take halarta lokacin da take Kiristanci.

Dattijuwa yar shekara 102 ta karbi Musulunci

A baya, kun ji cewa wani bidiyo mai taba zuciya ya karade intanet, ya nuna wata mata 'yar shekara 104 da ta karɓi Musulunci tana da shekaru 102.

A cikin rahoton, wani mutum ya bayyana cewa an haifi matar a 1940, kuma yana da katin shaidar ta domin tabbatar da hakan.

Duk da shekarunta, tana zuwa masallaci kullum daga safe har yamma, ta fi jin daɗin salla da jama'a fiye da yin ta ita kaɗai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.