Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Masu Yawa, An Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga a Kaduna

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Masu Yawa, An Cafke Hatsabibin Ɗan Bindiga a Kaduna

  • Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda masu yawa tare da ceto mutum 67 a hare-haren da suka kai a jihohi daban-daban
  • Rundunar ta kuma cafke mutane 94 da ake zargi, tare da kwato makamai kala kala da lalata sansanonin 'yan ta'adda
  • Dakarun soji dai na ci gaba da fatattakar miyagu a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Kudancin kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Dakarun rundunar tsaro ta Najeriya sun samu gagarumar nasara a makonni biyu da suka gabata, inda suka kashe 'yan ta'adda da dama.

Baya ga 'yan ta'addan da aka kashe, dakarun sojojin sun kuma samu damar ceto mutum 67 da aka sace, tare da kama wasu 94 da ake zargi da aikata laifuffuka.

Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda masu yawa, sun kuma kama wasu
Dakarun sojojin Najeriya suna rangadi a wasu sassan jihar Borno. Hoto: Audu Marte
Source: Getty Images

Ayyukan sojoji a cikin watan Nuwamba, 2025

Kara karanta wannan

ISWAP: Masu hidimar kasa, NYSC sun tsallake rijiya da baya a Borno

Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Olatokunbo Bello, ne ya bayyana hakan a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Olatokunbo Bello, ya bayyana cewa an samu nasarorin ne a ayyukan da sojoji suka gudanar daga 3 zuwa 14 ga Nuwamba, 2025.

A cewarsa, dakarun sojoji sun kwato bindigogi masu yawa, har da bindigogin zamani, manyan bindigogi, rokoki, bindigogi na gida, da kayan hada bam.

Hakazalika, Manjo Janar Olatokunbo Bello, ya shaida cewa sojoji sun kuma lalata sansanonin 'yan ta'adda da wuraren ajiyar kayayyakin su.

Nasarorin sojoji a Arewa maso Gabas da ta Yamma

A Arewa maso Gabas, sojojin Operation Hadin Kai sun ci gaba da fatattakar Boko Haram da ISWAP a Borno da Adamawa, inda suka hallaka ‘yan ta’adda da dama.

Manjo Janar Bello ya ce an kama mutane 45 da ke taimakawa ‘yan ta’adda da bayanai da kayan abinci, tare da ceto mutum ɗaya da aka yi garkuwa da shi.

A Arewa maso Yamma kuwa, Operation Fagge Yamma ta samu nasara a jihohi Sokoto, Zamfara, Niger, Katsina, Kebbi da Kano.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika, sojojin Najeriya sun kama mai sayar wa ƴan ta'adda makamai a Taraba

Sojojin sun kashe wasu ‘yan ta’adda, suka kama mutum biyu, tare da ceto mutum 13. An kuma kwato makamai, motoci da dabbobi.

Ayyukan sojoji a Arewa ta Tsakiya

A Arewa ta Tsakiya, Operation Enduring Peace ta dakile hare-hare a Plateau da Kaduna, inda aka kashe wasu miyagu, aka kama mutum 16, tare da ceto mutum biyar.

Haka kuma an kama fitaccen barawo, Ibrahim Wakili, a garin Sanga, Kaduna a ranar 9 ga Nuwamba, 2025, in ji rahoton Daily News.

A Operation Whirl Stroke kuwa, an samu nasara a Kogi, Kwara, Benue, Nasarawa da Taraba, inda aka kashe masu laifi, aka kama mutum 10, tare da ceto mutum 48.

Sojojin Najeriya sun ce sun ceto fiye da mutanr 50 da 'yan ta'adda suka yi garkuwa da su.
Hotunan wasu daga cikin wadanda sojojin Najeriya suka ceto daga hannun 'yan ta'adda. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Fatattakar masu satar mai da 'yan bindiga

A yankin Niger Delta, Operation Delta Safe ta dakile satar mai da ta kai kusan N15.8 miliyan, tare da lalata wuraren hada man fasa-kauri da kama mutum tara.

A Kudu maso Gabas, Operation Udo Ka ta kashe ‘dan ta’adda ɗaya, tare da kama wasu guda bakwai a jihohin Imo, Enugu, Akwa Ibom da Cross River.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya bai wa A.M Yerima kariya bayan takaddama da Wike

Manjo Janar Bello ya jinjinawa dakarun kan jajircewarsu, tare da kira ga kafafen yada labarai su ci gaba da yada sahihan bayanai domin taimakawa zaman lafiya da tsaron kasa.

Sojoji sun yi arangama da 'yan ta'adda a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 86 da aka yi garkuwa da su a tsakanin yankin Buratai–Kamuya, jihar Borno.

Rundunar soji ta musamman ta 135 da ke Buratai, ta rahoto cewa sojoji sun kai ahrin ne bayan samun sahihan bayanai kan motsin ‘yan ta’adda a hanyar Buratai–Kamuya.

Bayan wasu miyagu sun tsere, sojoji sun bi bayansu, har suka gano sansanin Boko Haram/ISWAP, inda a cikinsa aka ceto mutane 86, sannan aka kona shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com