'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dan Kasuwa kuma Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Dan Kasuwa kuma Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP

  • Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon shugaban PDP a mazabar Boriya/Shiya da ke karamar hukumar Buruten a jihar Kwara, Abubakar Sise
  • Majiyoyi daga yankin sun ce maharan sun bude wuta a sama don tsorata mutane, kafin daga bisani su tafi da shi zuwa cikin daji
  • Duk da har yanzu ba a san inda yan bindigar suka nufa ba, amma yan sa-kai sun naza komarsu domin ceto Alhaji Sise cikin koshin lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara, Nigeria - ’Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki cikin daren jiy Alhamis a jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya barke a APC, ana kokarin tilasta shugaban jam'iyya ya yi murabus

'Yan bindigar sun sace wani ɗan kasuwa kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na mazabar Boriya–Shiya a ƙaramar hukumar Baruten ta Jihar Kwara, Abubakar Sise.

Taswirar jihar Kwara.
Hoton taswirar jihar Kwara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tashar Channels tv ta tattaro cewa maharan sun sace Abubakar Sise ne daga gidansa da ke unguwar Boriya da sanyin safiya, tun kafin sallar asubahi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka sace tsohon shugaban PDP

Bayanai sun nuna cewa harin ya faru ne misalin ƙarfe 12 na dare, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye gidan, suna harbe-harbe a sama domin tsoratar da mazauna yankin.

Wasu majiyoyi sun ce ɗaya daga cikin ’ya’yan Alhaji Sise ya hadu da ’yan bindigar ba tare da sani ba yayin da yake dawowa gida da daddare, inda suka kama shi

An rahoto cewa ’yan bindigar sun tilasta masa ya kira mahaifinsa ya kuma buɗe musu ƙofa. Da suka shiga, sai suka tafi da mahaifin kawai, suka bar sauran ’yan gida lafiya.

Da safe, an tarar da kwankon harsashin bindiga a warwatse a cikin harabar gidan, abin da ya tabbatar da cewa an yi harbe-harbe da dama yayin harin.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da suka sa 'yan bindiga ke kara kaimi wajen kai hari Kano

Wane mataki jami'an tsaro suka dauka?

Mazauna yankin sun bayyana lamarin a matsayin hari na dan takaitaccen lokaci, amma kuma mai firgitarwa wanda bai ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin ’yan bindigar su tsere.

Jami’an sa-kai na yankin Boriya sun samu labari sace tsohon shugaban PDP, kuma sun fara bincike da sintiri a dazuzzukan da ke kusa domin gano inda maharan suka nufa tare da ceto wanda aka sace.

Wannan shi ne hari na biyu na garkuwa da mutune da aka samu a yankin cikin watanni biyu.

Shugaban PDP na kasa, Umar Damagum.
Hoton shugaban PDP na kasa, Umar Damagum. Hoto: PDP Nigeria
Source: Twitter

A ranar 17 ga Satumba, yan bindiga sun kai farmaki kuma suka sace wani ɗan kasuwa daga gidansa a unguwar Shiya, wanda ba shi da nisa da Boriya.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a iya gano inda Alhaji Abubakar Sese ya ke ba.

Yan bindiga sun sace mata 5 a Kano

A wani labarin, kun ji cewa ‘yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Yan Kwada da ke yankin Faruruwa a karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Bayanai sun nuna cewa 'yan ta'addan sun yi nasarar sace mata har guda biyar, ciki har da masu shawarwa a wannan hari.

Shaidun gani da ido sun ce maharan sun iso kauyen cikin tarin yawa, dauke da muggan makamai, suna harbe-harbe kafin su shiga gidaje domin yin garkuwa da mutanen da suka so.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262