'Yan Ta'adda Sun Kakaba Sababbin Haraji a Garuruwan Zamfara
- ’Yan bindiga sun kara jefa mazauna wasu garuruwa a jihar Zamfara a cikin sabuwar matsala da zaman dar-dar
- Sababbin rahotanni sun tabbatar da cewa yan ta'addan sun kakaba haraji mai a kan al’ummomin ƙauyuka a Tsafe, Zamfara
- Miyagun mutanen sun tilasta wa mazauna Danjibga biyan N8m, sannan an kara raba harajin a kan wadansu garuruwan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara – Rahotanni daga yankin Tsafe a Zamfara sun tabbatar da cewa 'yan ta;adda sun kara bijiro da hanyar zaluntar mazauna wasu garuruwan jihar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a halin da ake ciki, 'yan ta'addan sun dora haraji mai nauyi a kan garuruwa da dama a kauyukan Tsafe.

Source: Facebook
Bakatsine ya wallafa a shafin X cewa wannan na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da fama da tabarbarewar tsaro a arewa maso yammacin ƙasar.
'Yan ta'adda sun saka haraji a Zamfara
Majiyoyi masu tushe sun shaida cewa a Danjibga, ’yan bindigar sun kakaba wa al’umma haraji na N8m.
An ruwaito cewa 'yan ta'addan sun ce N4m diyya ce kan babura biyu da jami’an tsaro suka kwace daga hannunsu.
Sai kuma N4m da suka alakanta da wani kuɗi da suka yi zargin wani matashi daga yankin ya ɗauka daga gare su.
Don tilasta biyan kuɗin, ’yan bindigar sun tare mota dauke da buhuna 100 na wake tare da yin garkuwa da mutum huɗu.
Rahotanni sun ce an ci gaba da rike su har sai an tattara kuɗin da suka nema. Daga nan ne suka amince za su sako motar da mutanen bayan kammala biyan kuɗin.
Mazauna kauyukan Zamfara sun shiga matsala
Wannan haraji ba Danjibga kaɗai ya tsaya ba, domin ya yan ta'addan sun kara dora haraji a kan wadansu kauyukan da ke karamar hukumar Tsafe.
A Kagana, 'yan ta'adda sun dora masu N4m, Bare-Bari ma za su biya N4m, sai kuma Kurin Ganwa da aka dora masu N40m idan suna son zaman lafiya.

Source: Original
Mazauna yankunan sun bayyana cewa suna shan matsin lamba daga 'yan ta'adda, kuma hakan ya jefa su a cikin firgici sosai.
Sun yi kira ga gwamnatin Zamfara da hukumomin tsaro na ƙasa da su ɗauki mataki cikin gaggawa domin kare rayukansu.
Sun ce idan aka cigaba da jinkiri, akwai yiwuwar ƙarin al’ummomi da yawa su faɗa ƙarƙashin irin wannan harajin dole da kuma barazanar garkuwa da mutane.
An kashe 'yan ta'adda dga Zamfara
A baya, mun wallafa cewa awani gagarumin samame da jami’an tsaro suka kai, fiye da ’yan bindiga 80 sun gamu da ajalinsu yayin da suka yi yunkurin shiga Kebbi daga Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan artabu ya faru ne a dajin Makuku, inda dakarun hadin gwiwa suka yi wa ’yan bindigar ruwan wuta ta sama da ƙasa, har aka ci karfinsu.
An ce jiragen yaki na rundunar sojin sama da sojojin kasa sun fatattaki ’yan bindigar a sansanoninsu, lamarin da ya haifar da mummunar asara ga tawagar miyagun mutanen,
Asali: Legit.ng

