Da Gaske Donald Trump Ya Ce zai Cafke Bola Tinubu Cikin Sa'o'i 24?
- Wani rahoto ya yi ikirarin cewa shugaban Amurka Donald Trump ya lashi takobin cafke Shugaba Bola Tinubu cikin sa'o'i 24
- Bincike ya gano cewa dukkan rahotannin da suka yadu daga kafofin sada zumunta kan lamarin ba da daga hukuma suke ba
- Legit Hausa ta hada rahoto na musamman domin nazari kan zargin da aka jingina ga shugaban Amurka game da Bola Tinubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wani rahoto da ya yadu a kafafen sada zumunta ya bayyana cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi barazanar cafke shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Rahoton ya yi ikirarin cewa Trump ya ce zai cafke Bola Tinubu ne a cikin awa 24 ba tare da jami’an tsaronsa sun ankara ba.

Source: Getty Images
Wannan da’awar ta samo asali ne daga bidiyo da rubuce-rubuce da aka yada a shafin This is Bendel a Facebook, TikTok da wasu shafukan yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Asalin da’awar da abin ya samo tushe
A binciken da aka gudanar, an gano cewa rahoton ya fara bayyana ne a wani shafin YouTube mai suna NedMedia a ranar 7, Nuwamba, 2025.
Bidiyon, wanda aka riga aka kalla fiye da sau 70,000, ya ɗauki wani tsohon jawabin Trump, inda yake cewa Amurka za ta iya tura dakarunta su dakile ‘yan ta’adda masu kisa a Najeriya.
A wannan jawabin nasa, Trump ya yi magana ne dangane da zargin kisan kiyashi na kiristoci a Najeriya, amma bai ambaci shugaban Najeriya ko batun cafke shi cikin awa 24 ba.
Yadda aka kirkiri labarin cafke Tinubu
A bidiyon da NedMedia ta wallafa, mai gabatar da shirye-shirye ya nuna wani sakon X daga Mike Arnold, tsohon magajin gari a Texas, yana cewa Amurka na shirin kawar da Tinubu.
Sai dai bayan duba sakon X din da aka dogara da shi, ba a samu wani bayani da ke goyon bayan wannan fahimtar ba.
Bincike ya nuna cewa mai gabatarwar ne kawai ya yi fassara bisa hakan, ba tare da gabatar da wata hujja ba.
Haka kuma babu wata kafar yada labarai ta duniya ko ta cikin gida da ta wallafa labarin a matsayin magana kai tsaye daga Trump.
Babu kuma wani rubutu ko sanarwa a shafukan sada zumuntar Trump, ko a shafin Fadar White House da ke nuna cewa ya yi irin wannan barazana.
Sakamakon bincike kan labarin
Binciken da aka gudanar kan wannan batu ya nuna cewa dukkan rahotannin da ke cewa Trump ya yi barazanar cafke Tinubu cikin awa 24 ba su da tushe.
A dukkanin bayanan da suka fito daga majiyoyin hukuma, babu wata shaida da ke goyon bayan wannan da’awa.
The Cable ta rahoto cewa idan da hakan ta faru, da tabbas manyan kafafen yada labarai na duniya sun yi rubuce-rubuce a kai.

Source: Facebook
Fasto ya yi kira ga Trump kan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa wani fasto a Najeriya, Wale Oke ya yi magana kan sabanin fahimta da aka samu tsakanin Najeriya da Amurka.
Fasto Oke ya ce Najeriya ba ta bukatar kutse da shugaban Amurka ya yi barazanar yi domin cewa zai yaki 'yan ta'adda.
Ya yi kira ga shugaban Amurka da ya hada kai da Bola Ahmed Tinubu wajen magance matsalar tsaro maimakon masa barazana.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


