Tsohon Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan Ya Tsoma Baki kan Sabanin Wike da Yerima

Tsohon Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan Ya Tsoma Baki kan Sabanin Wike da Yerima

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bukaci ‘yan Najeriya su daina raina jami’an tsaro ganin yadda suka sadaukar da rayuwarsu
  • Ya bayyana haka ne bayan takaddamar jami'in sojan ruwa, A.M Yerima da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike a kan wani fili
  • Sanata Ahmad Lawan ya ce sojoji suna bayar da rayukansu don kasa, don haka dole ne a girmama su saboda girman sadaukarwar da suka yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja –Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji raina jami’an rundunar tsaro.

Ya bayyana cewa sadaukarwar da suke yi ya sa dole ne a ci gaba da nuna musu goyon baya da girmamawa.

Ahmad Lawan ya bada shawara kan alakar sojoji da jama'a
Hoton tsohon Shugaban majalisa Ahmad Lawan, Nyesom Wike Ministan Abuja Hoto: Ahmed Ibrahim Lawan/Lere Olayinka
Source: Facebook

Arise News ta wallafa cewa Sanata Ahmad Lawan ya yi wannan jawabi ne a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis bayan ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

A.M Yerima: Tsohon jigon APC, Frank ya shawarci Tinubu ya ja kunnen Wike

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmad Lawan ya nemi a girmama sojoji

Politics Nigeria ta wallafa cewa Ahmad Lawan ya ce yana da cikakkiyar shaida kan yadda sojoji ke sadaukar da rayukansu domin kare kasar.

Ya ce:

“Sojojinmu suna bada rayuwarsu don wannan kasa. Sun cancanci a ba su girmamawa tare da samun cikakken goyon bayan ‘yan kasa. Wannan gwamnati kuma na zuba jari sosai wajen inganta rundunar tsaro.”

Ahmad Lawan, wanda yanzu ke shugabantar kwamitin tsaro na majalisar dattawa, ya ce ‘yan Najeriya – komai matsayinsu – dole su nuna ladabi ga jami’an tsaro.

Ya nanata cewa jami'an tsaron da ake da su, su ne katangar kare kasar da al’ummarta daga dukkanin wata barazana da ke tunkaro wa.

Ahmad Lawan ya magantu kan kasafin kudi

Game da jinkirin aikawa majalisar dokoki kasafin kuɗin 2026, Ahmad Lawan ya ce babu wani abin damuwa a wannan batu.

Sanata Ahmad Lawan ya jinjina wa Bola Ahmed Tinubu
Hoton tsohon shugaban majalisar dattawa Hoto: Ahmed Ibrahim Lawan
Source: Facebook

Ya bayyana cewa bangarorin gwamnati biyu suna fahimtar muhimmancin kammala kasafin a kan lokaci domin amfanin al'umma.

Kara karanta wannan

ISWAP: Masu hidimar kasa, NYSC sun tsallake rijiya da baya a Borno

Ya ce:

“Lokaci na da muhimmanci idan ana magana kan kasafin kasa. Ina da tabbacin cewa bangaren zartarwa na kokarin kammala komai. Da zarar an gabatar, majalisa za ta bi shi, ta tantance shi, sannan ta amince ba tare da bata lokaci ba.”

Ahmad Lawan ya ce ya ziyarci shugaban kasa ne domin yaba wa Tinubu kan matakan da ya dauka a tsawon shekaru biyu wajen gyara tattalin arziki da karfafa tsaron kasa.

Ya ce tattalin arzikin kasar ya fara daidaituwa, kuma gwamnati na kara zuba jari a tsaro don magance matsalolin da suka rage.

Frank ya ba Tinubu shawara kan Wike

A baya, mun wallafa cewa Timi Frank, tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na APC, ya shawarci Bola Ahmed Tinubu a kan ya gargadi Ministan Abujam Nyesom Wike.

Wannan na zuwa ne bayan wani faifan bidiyo da ya yadu a ranar Talata, inda aka ga sojoji sun dakatar da Wike da tawagarsa daga shiga wani fili da ake cece-kuce a kai a Abuja.

Kara karanta wannan

Ana batun matashin soja da Wike, Tinubu ya yi magana kan jarumtar sojojin Najeriya

Timi Frank ya bayyana cewa halin da Wike ya nuna, alama ce na cewa ana mulki da iko a gwamnatin Tinubu, lamarin da ya ce bai dace da mulkin dimokuradiyya ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng