Lamari Ya Munana: Majalisa Ta Bukaci Gwamnatin Tinubu Ta Sassauta Farashin Taki
- Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta dauki mataki game da tsadar takin zamani da kayan noma
- Majalisar ta bukaci rage farashin saboda yadda yake cutar da manoma da kuma jawo musu asara mai yawa
- Dan majalisa Yusuf Galambi ya ce hauhawar farashin taki na rage samar da abinci da jefa manoma cikin matsin tattalin arziki da karancin amfanin gona
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar Wakilai ta Najeriya yayin zamanta ta tura roko na musamman ga gwamnatin tarayya kan takin zamani wanda ke kara tsadar abinci.
Majalisar a ranar Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025 ta bukaci Gwamnatin Tarayya ta rage farashin takin zamani da sauran kayan noma.

Source: Facebook
An bukaci gwamnati ta rage farashin taki
Wannan ya biyo bayan gabatar da kudirin da dan majalisa Yusuf Galambi ya gabatar a majalisar a yau Alhamis 13 ga watan Nuwambar 2025, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yusuf Galambi ya nuna damuwa game da tsadar takin zamani a kasuwa wanda ya ke jefa manoma cikin masifa da kuma asara mai tarin yawa.
Galambi ya ce noma na da matukar muhimmanci ga samar da abinci da ci gaban tattalin arziki, amma yana bukatar taki da kayan noma masu saukin farashi.
Ya bayyana cewa taki da kayan noma suna taimakawa wajen kara lafiyar kasa da amfanin gona, don haka suna da muhimmanci wajen habaka samar da abinci.

Source: Facebook
Matsalar tsadar takin zamani, kayan noma
Majalisar ta nuna damuwa cewa karin farashin taki da sauran kayan noma na iya rage yawan amfanin gona da haifar da karancin abinci a kasar.
Galambi ya kuma ce hauhawar farashin wadannan kayayyaki na iya shafar noman damina da na rani, wanda hakan ke barazana ga tsaron abinci.
Ya kara da cewa yawancin sassan kasar na fama da karancin abinci, yayin da hauhawar farashi ke sa kayan masarufi su zama masu tsada ga talakawa.
Yadda ake sayar da takin zamani a kasuwanni
Majalisar ta lura cewa duk da matakan gwamnati wajen daidaita farashin abinci, kayan noma kamar taki suna da tasiri wajen kara tsadar kayayyaki duba da halin da ake ciki.
A cewar rahoton kasuwa, buhu daya na taki mai nauyin kilo 50 tana sayarwa N60,000, wanda masana suka ce shi ne mafi tsada cikin shekaru 10 da aka taba samu.
Saboda haka, majalisar ta bukaci Ma’aikatar Noma da Tsaron Abinci ta dauki mataki don rage farashin taki da kayan noma domin tallafa wa manoma.
Majalisa na son ana amfani da motocin lantarki
An ji cewa Majalisar Dattawa ta amince da dokar sauya motocin man fetur zuwa na wutar lantarki domin kare muhalli da haɓaka masana’antun cikin gida.
Sanata Orji Kalu ne ya gabatar da kudirin, wanda ke neman kafa tsari domin samar da motocin wutar lantarki da samar da ayyuka masu yawa da rage talauci.
Rahoto ya ce kudirin ya tanadi rangwamen biyan haraji da sauye-sauyen shigo da kaya, tare da wajabta kafa wuraren cajin mota a fadin Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

