Gwamnatin Tinubu Ta Yi Gyaran Doka, Za a Koma Koyar da Dalibai Karatu da Yare 1
- Gwamnatin tarayya ta soke dokar koyarwa da harshen gida a makarantu, ta mayar da Turanci a matsayin harshen koyarwa kawai
- Ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya ce bincike ya nuna daliban da ake koyarwa da harsunan gida sun fi faduwa a jarabawa
- Yahaya Lawal Mailafia, shugaban makarantar firamare ta al'umma da ke Funtua, ya ce wannan mataki zai sake inganta ilimi a kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta soke dokar da ke wajabta koyar da dalibai da harsunan gida a makarantun Najeriya.
Gwamnatin tarayyar ta dawo dawo da Turanci a matsayin harshen koyarwa daga matakin firamare har zuwa jami’a.

Source: Getty Images
Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a taron kasa da kasa kan harshe da ilimi da Majalisar Birtaniya ta shirya a Abuja a ranar Laraba, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan soke dokar koyarwa da harshen gida
Ya ce an amince da soke manufar ne a taron majalisar ilimi ta kasa (NCE) karo na 69 da aka gudanar a Akure, jihar Ondo, daga 3 zuwa 7 ga Nuwamba, 2025.
A 2022, muka ruwaito cewa, gwamnati ta yi doka cewa za a rika koyar da dalibai daga matakin karatu na ECE zuwa aji shida na firamare da harshen gida.
Sai dai Dr. Alausa ya ce bayanai sun nuna cewa wannan tsarin bai yi wani tasiri na inganta ilimi ba, maimakon haka ya jawo koma baya a wasu yankuna.
“Mun ga yawan faduwar dalibai a jarabawar WAEC, NECO, da JAMB a wasu yankuna, musamman inda aka fi amfani da harshen gida wajen koyarwa.
“Wannan gwamnati tana aiki bisa hujja, ba jin kai ba. Saboda haka, Turanci ne zai kasance harshen koyarwa daga matakin firamare har zuwa jami’a.”
- Dr. Tunji Alausa.

Kara karanta wannan
Rigima da soja: Kungiya ta bukaci Tinubu ya kori Wike, ta fadi wanda ya kamata ya maye gurbinsa
Alausa: “Harshen gida ya lalata ilimi”
Ministan ya ce amfani da harshen gida a makarantu cikin shekaru 15 da suka gabata ya rage ingancin fahimta da sakamakon karatu a yankuna da dama.
Ya bayyana cewa daliban da ake koyarwa da harshen gida suna samun matsala wajen karatu da fahimtar Turanci, wanda ke kawo cikas a jarabawa ta kasa da kasa.
“Dole mu dogara da shaidu. Idan akwai wanda ke da hujja, gwamnati za ta saurare shi, amma ilimi wani abu ne da yake bukatar ya yi daidai da zamani."
- Dr. Tunji Alausa.

Source: Twitter
Gwamnati na buɗe kofa ga sababbin shawarwari
Dr. Alausa ya bukaci masu ra’ayin da ya saba wa gwamnati da su gabatar da sahihan bayanai don nuna amfanin koyarwa da harshen gida.
Ministan ilimi ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta ci gaba da tattaunawa da masana bisa hujja don kawo gyara a fannin ilimi.
Ya kuma gode wa Majalisar Birtaniya saboda haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya wajen bunkasa tsarin ilimi da inganta dabarun koyarwa a harshen Turanci.
'Wannan mataki ya yi dai dai' - Shugaban makaranta
A zantawar Legit Haua da Yahaya Lawal Mailafia, shugaban makarantar firamare ta al'umma da ke Funtua, jihar Katsina, ya ce wannan mataki zai sake dora ƙasar a lokacin dauri.
Yahaya Lawal ya ce mafi akasarin wadanda ake ganin sun taka duk wani matsayi da suka taka, sun yi hakan ne saboda irin ilimin da suka samu, kuma an koyar da su ne a Turanci zalla.
"Idan muka kalli kasar da ta yaye mu, za mu ga Baturiya ce, shi ya sa mu yaren koyarwar mu ya zama Turanci, a lokacin Turawan ne da kansu suka koya masu.
"To yanzu da aka rika sirkawa da Hausa, sai ya zamana cewa Turancin ya fara barin bakinmu. Malami ba zai yi magana da Turanci ba, haka dalibansa, alhalin littattafai da bincike duk an yi su da Turanci ne."
- Yahaya Lawal.
Shugbana makarantar ya ce akwai abubuwna da ba za a iya yin bayaninsu da yaren uwa ba, dole sai da Turanci, don haka rashin iya Turanci na cutar yara tun daga matakin Firamare.
Ya ce yana goyon bayan wannan mataki na gwamnatin Taryaya, domin a cewarsa, hakan zai sake dawo da martabar ilimi, hazakar dalibai da kuma gogayya da kasashen waje.
Za a tilasta koyarwa da Hausa a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar dokokin Kano ta fara duba kudurin doka da zai wajabta koyarwa da harshen gida, musamman Hausa.
Hon. Musa Ali Kachako ne ya dauki nauyin kudurin wanda ya ce zai taimaka wajen inganta fahimtar dalibai da rage faduwa a jarrabawa.
Kudurin ya shiga hannun Kwamitin Ilimi na majalisar dokokin domin karin nazari da bayar da shawarwari kafin karatun sa na gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

