Manyan Jiragen Ruwa 20 Makare da Man Fetur da Kayan Abinci Sun Iso Najeriya

Manyan Jiragen Ruwa 20 Makare da Man Fetur da Kayan Abinci Sun Iso Najeriya

  • Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya ta ce jiragen ruwa 20 na sauke fetur da kayan abinci a tashoshin Legas
  • Bayan fetur, kayayyakin abinci da jiragen ke sauke wa sun hada da daskararren kifi, sukari, taki, gas, da kayan masarufi
  • A cikin mako guda, ana sa ran ƙarin jirage 20 za su isa tashoshin Lekki, Tincan, Apapa, domin sauke kayayayyaki da fetur

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA) ta tabbatar cewa jiragen ruwa 20 makare da tataccen man fetur da kayan abinci sun iso Legas.

Hukumar NPA ta bayyana cewa yanzu haka jiragen suna kan aikin sauke man fetur da kayan abinci a tashoshin jiragen ruwa na Apapa, Tincan Island, da Lekki, a jihar Legas.

Kara karanta wannan

DSS ta tafi kotu da wanda ya nemi a yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

Jiragen ruwa dauke da fetur da kayan abinci sun fara sauke kayayyaki a Legas.
Tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke birnin Legas. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Jiragen ruwa makare da fetur da abinci sun iso Legas

Wannan bayani ya fito ne daga rahoton hukumar wanda aka fitar ranar Laraba a birnin Legas, kuma aka raba wa 'yan jarida, ciki har da kamfanin dillancin labarai (NAN).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukukumar NPA ta bayyana cewa kayayyakin da ake saukewa a halin yanzu sun haɗa da daskararren kifi, man fetur, sukari, da kuma urea.

Sauran kayayyakin da ake sauke wa daga kan jiragen sun hada da alkamar buckwheat, iskar gas, taki, da kayan masarufi.

Har ila yau, an ce wasu jirage biyu sun iso tashar, suna kuma jiran izinin fara sauke kayan da suka dauko, ciki har da alkama da kwantena.

Ana sa ran ƙarin jirage 20 zuwa 14 ga Nuwamba

Hukumar NPA ta kuma sanar da cewa ana sa ran zuwan ƙarin jirage 20 a tashoshin jiragen ruwa na Legas daga 12 zuwa 14 ga watan Nuwamba, dauke da kayayyaki da albarkatun mai.

Kara karanta wannan

Matsalar sufurin Amurka ta yi kamari, Trump ya yi wa ma'aikata barazana

Kayayyakin da ake sa ran za su iso da su sun haɗa da mai, man jirgin sama, dizal, gas, urea, sukari da kayayyakin abinci.

NPA ta ce wadannan jiragen na cikin tsarin samar da wadatar man fetur da abinci a kasar, don tallafa wa tattalin arziki da tabbatar da dorewar kasuwanci a cikin gida.

Rahoto ya nuna cewa jiragen ruwa makare da fetur da kayan abinci sun iso Legas.
Jiragen ruwa suna sauke kayayyaki a tashar jiragen ruwa ta Legas. Hoto: @nigerianports/X
Source: UGC

Rahotanni da suka gabata na zuwan jiragen ruwa

A makon da ya gabata, hukumar ta sanar da cewa jirage 17 ake sa ran isowarsu tsakanin 3 zuwa 7 ga Nuwamba, 2025 a tashoshin Apapa da Tincan.

Hukumar ta bayyana cewa jirage 13 daga ciki na ɗauke da albarkatun man fetur, yayin da hudu suka ɗauko kwantena na kayayyaki, in ji rahoton The Nation.

A wancan lokacin, jirage 16 suna sauke kaya da suka haɗa da kifi, alkama, gas, da kayan masarufi, yayin da jirage 6 ke jiran sauke kayan da suka dauko.

Rahoton ya nuna cewa ayyukan sauke kaya a tashoshin Lagos na ci gaba cikin tsari, wanda ke taimakawa wajen wadatar kayan abinci, man fetur da kasuwanci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tirkashi: EFCC ta kafe hoton Timipre Sylva, ana neman tsohon gwamna ruwa a jallo

Dangote zai gina tashar jiragen ruwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana shirin gina tashar jiragen ruwa da fadada kamfanin siminti a Jihar Ogun.

Dangote ya ce tashar ruwa da zai gina za ta zama mafi girma a Najeriya, kuma za ta farfado da shirin da aka yi watsi da shi a yankin Olokola.

A cewarsa, sabuwar tashar jiragen ruwan za ta zama wata babbar hanyar sauƙaƙa fitar da kayayyaki daga Najeriya zuwa kasashen waje.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com