Atiku Ya ba Matashin Sojan da Ya Yi Rigima da Wike Kyautar Sabuwar Mota? Gaskiya Ta Fito
- Wani rahoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta ya nuna cewa Atiku Abubakar ya ba matashin soja, A M Yerima kyautar mota
- Labarin ya fara yawo ne bayan takaddamar da ta faru tsakanin Yerima da ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike a ranar Talata
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya fito ya musanta labarin, yana mai cewa babu wanda ya ba kyautar mota a kwanan nan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigera - A yammacin jiya Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025 wani rahoto ya fara yawo cewa Atiku Abubakar ya ba matashin soja, A. M Yerima kyautar mota.
Rahoton wanda cikin kankanin lokaci ya karade kafafen sada zumunta, ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa ya ba sojan kyautar mota Prado saboda rikicinsa da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Source: Twitter
Yadda aka fara jita-jitar kyautar mota
Abba Sani Pantami na cikin wadanda suka wallafa wannan jita-jita a Facebook, tare da jingina labarin ga daya daga cikin hadimin Atiku Abubakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Atiku Abubakar ya ba matashin soja, A.M Yerima, kyautar sabuwar mota kirar Prador 2024, ya kuma yi kira ga rundunar sojojin Najeriya da ta karawa matashin sojan girma tare da karrama shi," in ji rahoton.
An dai samu rikicin ne ranar Talata, lokacin da Wike ya je duba wani fili da ake takaddama kansa a yankin Gaduwa, inda ya yi sa-in-sa da Lafatanal Yerima, wanda ya dage cewa yana bin umarni daga sama.
Dagaske Atiku ya ba Yerima kyauta?
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya fi karyata labarin da ke cewa ta bai wa Laftanal Ahmad Yerim, matashin sojan ruwan da ya yi takaddama da Wike kyautar mota.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai ba Atiku shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X yau Alhamis, 13 ga watan Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan
Ana batun matashin soja da Wike, Tinubu ya yi magana kan jarumtar sojojin Najeriya
Paul Ibe ya bayyana labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsagwaronta, wacce ba ta hujja balle makama.
Ibe ya roƙi jama’a da su yi watsi da wannan labari, yana mai cewa:
"Atiku Abubakar, wanda ya kasance Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1999 zuwa 2007, bai bai wa Lt. Ahmed Yerima ko wani mutum dabam wata sabuwar Toyota SUV ba, kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta.
"Wannan labari gaba dayansa ƙirƙirarre ne, don haka jama’a su yi watsi da shi baki ɗaya.”

Source: Facebook
Hadimin Shettima ya kare Wike
A baya, kun ji labarin cewa Gimba Kakanda, hadimin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kare karfin ikon ministan Abuja, Nyesom Wike.
Kakanda ya ce karfin ikon Wike kan filayen Abuja ya tabbata bisa doka, kuma duk wani yunƙuri daga sojoji na toshe wannan iko, na nufin karya dokar kundin tsarin mulki.
Ya bayyana cewa korafin da ake yi da kiran Wike da mai kwacen filaye ba shi da hujja, domin bisa doka, ministan Abuja yana da iko daidai da na gwamnonin jihohi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
