Tinubu: Fasto Ya Tura Sako ga Trump kan Kashe Kashe da ake a Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa Cocin PFN ya yi kira ga shugaban Amurka, Donald J. Trump kan dakile kashe-kashe a Najeriya
- A baya dai Legit Hausa ta rahoto cewa Trump ya yi barazanar kai farmaki Najeriya bisa zargin kisan Kiristoci da yawa
- Sai dai gwamnatin tarayya ta karyata zargin, ta ce rikice-rikicen tsaro ba na addini ba ne, kuma tana daukar mataki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Cocin PFN ya yi kira ga shugaban Amurka, Donald Trump, da ya hada kai da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wajen magance matsalar tsaro.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa shugaban PFN, Bishop Wale Oke ne ya bayyana haka.

Source: Getty Images
Ya yi kira ga Trump ne a hirar da ya yi da tashar Channels TV a ranar Alhamis, inda ya jaddada cewa rayuwar kowane dan Najeriya tana da muhimmanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kiran PFN ga shugaba Trump
Faston ya ce PFN ba ta goyon bayan kowane irin kutsen soji daga waje, sai dai hadin gwiwa da gwamnatin Najeriya don samun shawarwari da horo kan yaki da ta’addanci.
Bishop Wale Oke ya ce:
“Abin da muke so shi ne a dakatar da kashe-kashe. Rayuwar kowane dan Najeriya tana da daraja.
"Idan shugaba Tinubu yana bukatar taimakon Amurka wajen horo ko dabaru kan yaki da ta’addanci, ya kamata a nemi hakan cikin hadin kai.”
Ya kara da cewa:
“Ba ma son Amurka ta kawo sojojinta Najeriya. Muna son Donald Trump ya yi aiki tare da Shugaban mu wajen tabbatar da cewa ana kare rayuka, ana kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa musamman kan mabiya addinin Kirista.”
Wannan jawabin na PFN ya biyo bayan barazanar kai farmaki da Donald Trump ya yi, inda ya bayyana cewa za a dauki matakin soja idan Najeriya ba ta kawo karshen kashe-kashen Kiristoci ba.
A cikin sakonsa, Trump ya rubuta cewa:
“Kiristanci na fuskantar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci. Masu tsattsauran ra’ayi ne ke da alhakin wannan kisan.”
Bayan wannan barazanar, Trump ya umarci ma’aikatar tsaronsa da ta fara shirin kai farmaki, abin da ya jawo martani daga gwamnatin Najeriya.

Source: Twitter
Kiran PFN ga shugaba Bola Tinubu
Bishop Wale Oke ya sake jaddada cewa PFN ba ta son kutse, amma tana son ganin an kawo karshen kashe-kashen da ke addabar ‘yan kasa.
“Muna son kowa — Musulmi ko Kirista — ya samu ‘yancin rayuwa, aiki da ibada ba tare da tsoro ko wariya ba a duk sassan Najeriya,”
Inji shi
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Tinubu da ta dauki matakan gaggawa don tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da hadin kai tsakanin al’ummar Najeriya baki daya.
Najeriya ta musa zargin Donald Trump
A wani labarin, ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce zargin da Trump ya yi ba shi da tushe, kuma yana nufin rarraba kawunan ‘yan kasa.

Kara karanta wannan
Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Ya ce ba gaskiya ba ne a nuna cewa matsalolin tsaro a Najeriya yana shafan wani rukuni na addini ne kawai.
Gwamnatin ta bayyana cewa ana samun nasarori wajen yaki da ‘yan ta’adda, kuma ta bude kofa ga kasashen duniya su bada taimako ta fuskar fasaha da horo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

