Hadimin Kashim Shettima Ya Fadi 'Mai Gaskiya' tsakanin Wike da Matashin Soja, A.M Yerima
- Gimba Kakanda, hadimin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kare karfin ikon ministan Abuja, Nyesom Wike
- Hadimin Shettima ya tsoma baki kan takaddamar da ta faru tsakanin Wike da matashin sojan ruwa lokacin da ministan ya je duba fili
- Kakanda ya bayyana cewa, Dokar Amfani da Ƙasa ta bai wa ministan Abuja irin ikon da gwamnoni ke da shi a jihohinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Takaddamar da ta auku tsakanin Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike, da jami’in sojin ruwa, Ahmad Yerima, a Abuja na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.
Gimba Kakanda, babban mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, kan harkokin bincike da nazari, ya fito da sababbin bayanai kan batun.

Source: Twitter
Kakanda ya yi bayanin ikon da doka ta bai wa Wike a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook, yana mai cewa babu wata hujja a doka ta sukar Wike, illa ƙiyayya ta siyasa da son zuciya.

Kara karanta wannan
A.M Yerima da Wike: Jerin mutane 4 da ke da karfin ikon bai wa soja umarni a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Shettima ya kare Wike
Ya bayyana cewa korafin da ake yi da kiran Wike da mai kwacen filaye ba shi da hujja, domin bisa doka, ministan Abuja yana da iko daidai da na gwamnonin jihohi wajen kula da harkokin ƙasa.
Kakanda ya ce karfin ikon Wike kan filayen Abuja ya tabbata bisa doka, kuma duk wani yunƙuri daga sojoji na toshe wannan iko, na nufin karya dokar kundin tsarin mulki.
Kakanda ya bayyana cewa waɗanda ke goyon bayan abin da A. M Yerima ya yi, dole su bayyana inda dokar rundunar soji ta amince da bin umarnin da bai dace ba sannan har mutum ya kare kansa da hujjar bin umarnin manya.
Dokokin da suka nuna Wike ke da gaskiya
Yayin da yake nuni da Sashe na 5 na Dokar Amfani da Ƙasa, hadimin Shettima ya ce gwamnonin jihohi da ministan Abuja suna da ikon yanka filaye, gudanar da su, da kuma soke mallaka domin amfanin jama’a.
Ya ƙara da cewa dokar ta ba su damar bayar da takardun mallaka, sanya tara ga masu karya ƙa’ida, da kuma sake duba ko sauya wasu sharuɗɗa idan akwai buƙata.
Kakanda ya ce sashe na 28 na Dokar Land Use Act ya ba da damar soke mallakar ƙasa idan akwai buƙatar jama’a, yayin da Sashe na 47 ke kare ikon Minista daga tsoma bakin kotu.
“Babu irin wannan umarni daga kotu yanzu, don haka duk wani matakin Minista yana kan bisa doka,” in ji Kakanda.

Source: Facebook
Ya yi gargaɗi cewa babu wanda ke da ikon mallaka ko gina ƙasa a Abuja ba tare da bin tsari da samun amincewar Minista ba, yana mai cewa duk wanda aka yi babu izini bai da amfani.
A ƙarshe, Kakanda ya amince cewa fitowar Wike da kansa zuwa wurin rikicin ba dole ba ne, amma doka ta ba shi cikakken iko.
Tsofaffin sojoji sun soki Ministan Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa tsofaffin janar-janar na rundunar soji sun nuna fushinsu kan rikicin da ya faru tsakanin ministan Abuja, Nyesom Wike, da wani soja, A. M Yerima.
Manyan sojojin da suka yi ritaya sun yi Allah wadai da irin martanin da Wike ya yi wa matashin sojan, wanda ya hana shi shiga waani fili da ake gina wa a Abuja.
Sun ce irin wannan lamari yana rage mutuncin gwamnati a idon duniya, kuma idan ba a yi tir da shi ba, zai iya gurbata tunanin dakarun da ke kare ƙasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

