Bayan Rikicin Manoma da Makiyaya, Gwamnati Ta Dakatar da Sarakuna 2 a Gombe
- Majalisar tsaro ta jihar Gombe ta dakatar da sarakuna biyu bisa gazawar hana rikicin manoma da makiyaya
- An ce rikicin da ya jawo aka dakatar da su ya yi sanadin mutuwa da lalata gonaki a yankin Funakaye
- Gwamnati ta ce bincike yana ci gaba, kuma matakin dakatarwar na ɗan lokaci ne har sai an kammala bincike
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Gwamnatin Jihar Gombe ta sanar da dakatar da sarakunan gargajiya biyu — hakimi da dagaci.
An dakatar da su ne bisa zargin gazawar su wajen hana rikicin manoma da makiyaya da ya faru a yankin ƙaramar hukumar Funakaye, wanda ya janyo asarar rayuka da dukiya.

Source: Facebook
Rahoton Punch ya nuna cewa an bayyana haka ne yayin zaman majalisar tsaro da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar.
Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan jihar, Barista Zubair Umar, ya tabbatar da dakatatar da masu rike da sarautar.
Dalilin dakatar da sarakuna a Gombe
A cewar Zubair Umar, majalisar ta tattauna kan yadda rikicin manoma da makiyaya ya sake kunno kai a wasu sassan jihar.
Ya ce an yanke hukuncin dakatar da shugabannin gargajiya biyu da ake ganin sun gaza wajen daukar mataki a kan lokaci.
Kwamishinan, Zubair Umar ya ce:
“An gabatar da rahoton sake barkewar rikicin manoma da makiyaya a wasu yankunan jihar Gombe ga majalisar tsaro, kuma bayan tattaunawa, an yanke hukuncin dakatar da shugabannin gargajiya biyu — dagaci da hakimi.”
Ya ce majalisar ta duba cewa rashin daukar mataki da wuri daga wadannan shugabanni ya taimaka wajen haifar da rikicin da ya faru a Funakaye.
“Ina so in jaddada cewa wannan mataki na dakatarwa an dauke shi ne domin zama izina ga sauran shugabannin gargajiya su rika taka rawar da ta dace wajen hana tashin hankali a yankunansu,”
Inji shi
Kwamishinan ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma bayan kammalawa za a sanar da sakamakon ga jama’a domin tabbatar da adalci ga kowa.

Source: UGC
Majalisar sarakuna ta yi karin bayani
A nasa bangaren, Mataimakin shugaban majalisar sarakuna, Mai Kaltungo, Alhaji Saleh Mohammed, ya bayyana cewa dakatarwar da aka yi wa dagacin da hakimin ba ta gaba daya ba ce.
Tribune ta rahoto ya ce:
“Wannan dakatarwa ba kora daga aiki ba ce, sai dai mataki ne na ɗan lokaci da aka ɗauka har sai an kammala bincike.
Mai Kaltungo ya yi kira ga manoma da makiyaya da su zauna lafiya da juna, tare da guje wa duk wani abu da zai iya janyo sabani.
Ya ce:
“Jihar Gombe na daga cikin mafi zaman lafiya a Najeriya, kuma wannan ne abin da muke son ci gaba da kiyayewa.”

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: 'Yan majalisa sun fara shiri, za su tsige shugaban majalisa a Ondo
Legit ta tattauna da Muh'd Rabiu
Rahotonnin da Legit Hausa ta samu ba su nuna hakikanin garin da aka dakatar da sarakunan ba a karamar hukumar Funakaye.
Sakamakon haka, Legit ta tattauna da wani da ke garin Komi da ke karamar hukumar ganin an yi rikicin manoma da makiyaya da ya jawo asarar rayuka.
Muhammad Rabiu ya ce:
"Tabbas an samu rikicin manoma da makiyaya a Komi, amma har yanzu ba mu samu labarin isar takardar dakatar da shugabannin ba a hukumance.
"Sai hukuma ta mika takarda kafin mu tabbatar da hakan."
Kwamishinan tsaron ya rasu a Gombe
A wani labarin, mun kawo muku cewa kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Gombe ya rigamu gidan gaskiya.
Rahotanni sun bayyana cewa kwamishinan ya rasu ne tare da dan sandan da ke tsaronsa a wani hadarin mota.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya mika ta'aziyya ga gwamnatin jihar bisa rashin.
Asali: Legit.ng

