Gwamna Yari ya dakatar da Sarakunan Gargajiya 4 a jihar Zamfara

Gwamna Yari ya dakatar da Sarakunan Gargajiya 4 a jihar Zamfara

Mun samu cewa gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Abubakar Yari, ya dakatar da wasu masu daurin rawani 4 bisa zargin hannunsu cikin ta'addancin satar shanu da kuma garkuwa da mutane da ya yi kamari cikin wasu sassa na jihar.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito da sanadin binciken manema labarai na jaridar BBC, gwamnatin jihar ta dakatar da wannan Sarakuna bisa zarginsu da mu'amala da kuma akala da 'yan ta'adda da ke tayar da zaune tsaye a jihar.

Kwamishinan ma'aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da kuma Masarautu na jihar, Alhaji Bello Dankande, shine ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Gusau a jiya Litinin.

Gwamna Yari ya dakatar da Sarakunan Gargajiya 4 a jihar Zamfara
Gwamna Yari ya dakatar da Sarakunan Gargajiya 4 a jihar Zamfara
Asali: Depositphotos

Alhaji Dankande ya bayyana jerin masu rawani da hukuncin dakacin ya shafa da suka hadar da Dagacin garin Gora da kuma na garin Barikin Daji da ke karkashin karamar hukumar Talata Mafara.

Sauran Iyayen kasar da lamarin ya shafa sun hadar da Mai garin kauyen Gyado da kuma na kauyen Tungan Dutsi da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Kwamishinan ya kara da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan dukkanin Sarakunan hudu inda za su gurfana gaban Kuliya yayin tabbatar da zargi akan su.

KARANTA KUMA: Kisan Dakarun Soji: Ya zama wajibi Majalisar Tarayya ta zurfafa bincike - PDP

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta daura damarar warware rawanin duk wani Basarake da bincike ya tabbatar da alaka ko mu'amalarsa da 'yan ta'adda.

Kamfanin Dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, jihar Zamfara a halin yanzu na ci gaba da fuskantar barazanar rashin tsaro musamman ta'addancin fashi da makami, garkuwa da mutane kashe-kashe da zubar jinin al'umma gami da satar shanu a yankunanta na karkara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel