Dubu Ta Cika, Sojojin Najeriya Sun Kama Mai Sayar wa Ƴan Ta'adda Makamai a Taraba
- Sojojin Najeriya sun cafke wani mai safarar makamai ga 'yan ta'adda a yayin samamen Operation Lafiya Nakowa a Taraba
- Rundunar ta ce an kama Abdulmudallabi Audu, mai shekaru 25, a Shagada, Gassol, dauke da bindiga da tulin harsasai
- Janar Kingsley Uwa ya yaba da aikin dakarun, yana mai cewa rundunar za ta ci gaba da murkushe ‘yan bindiga a kasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Sojojin Brigade ta 6 na rundunar sojin Najeriya da ke karkashin Operation Whirl Stroke sun samu asarar gurgunta ayyukan 'yan ta'adda a Taraba.
Rundunar sojin Brigade ta 6 ta bayyana cewa dakarunta sun kama wani mutum da ake zargin mai safarar makamai ne, kuma an same shi da bindigar AK-47 da harsasai 53.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta rahoto cewa sojoji sun gudanar da samamen ne a ƙarƙashin aikin Operation Lafiya Nakowa a ranar 12 ga Nuwamba, 2025, a kauyen Shagada, cikin gundumar Namnai, karamar hukumar Gassol.
Taraba: Sojoji sun kama mai safarar makamai
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Laftanar Umar Muhammad, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojin Brigade ta 6, ya fitar ranar Laraba.
Laftanal Umar Muhammad ya ce sojojin sun kai samamen ne bayan samun sahihin bayanan sirri daga mazauna yankin.
Sanarwar ta ce:
“An kama wanda ake zargi, Abdulmudallabi Audu, mai shekaru 25, a lokacin da ake gudanar da samamen. An same shi da bindigar AK-47, da harsasai 53.”
A cewarsa, an kwashe wanda ake zargin tare da kayan da aka kwato zuwa hedkwatar Brigade ta 6 domin ci gaba da bincike da kuma yuwuwar gurfanar da shi gaban kuliya.
An jinjinawa dakarun da suka kai samame
Brigadier Janar Kingsley Uwa, kwamandan Brigade ta 6, ya yabawa dakarun saboda kwazo da saurin kai samamen da suka yi bayan samun bayanan sirri.
Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman domin kawar da masu laifi, masu safarar makamai, da sauran masu aikata miyagun ayyuka a Taraba.
Jaridar Sun ta rahoto Janar Kingsley Uwa ya nemi mazauna yankin da su ci gaba da ba da sahihan bayanai ga jami’an tsaro domin taimaka musu wajen kawarda ‘yan ta’adda.

Source: Original
Hedkwatar soji ta tabbatar da tsaro a kasa
A wani labari mai alaka da wannan, Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tsaro zai inganta a makonni masu zuwa.
Jaridar The Nation ta rahoto Laftanar Janar Waidi ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar Aso Rock, Abuja, inda ya ce:
“’Yan Najeriya su yi hakuri, za a ga tsaro ya inganta nan ba da jimawa a duk fadin kasar nan.”
Hafsan sojin kasan ya ce ganawarsa da Tinubu na da alaka da ayyukan sojoji da ake gudanarwa a Arewa maso Gabas da yadda za a inganta tsaro a kasar.
Zamfara: An kama mai safarar makamai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata mata mai safarar makamai a jihar Zamfara ta shiga hannun jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Kara karanta wannan
Ba sauki: Jiragen yakin sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a jihohin Arewa 3
Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke matar ne dauke da kayan laifin wadanda ake zargin ta shirya kai su ga 'yan bindiga da ke cikin daji.
An ce matar ta fito ne daga karamar hukumar Birnin Magaji, inda aka gano harsasan a cikin kayanta lokacin da jami’an NDLEA suka dakatar da ita domin bincike.
Asali: Legit.ng

