Gumi Ya Yi Zargin ana Ƙona Akwatunan Gawa don Ƙaryar ana Kashe Kiristoci a Najeriya
- Sheikh Ahmad Gumi ya ce an gaya masa cewa wasu Kiristoci sun daga a kan lallai sai sun nuna wa duniya cewa ana kashe su a Najeriya
- Malamin ya bayyana cewa ya samu bayanan yadda wadansu kiristoci ke kona akwatunan gawa, suna binne wa da sunan 'yan uwansu
- Ya yi wannan zargi ne a lokacin da Najeriya ke kokarin tabbatar wa Amurka cewa matsalar tsaron kasar nan bai shafi addini ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Fitaccen malamin addini daga Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ya samu labari daga yadda ake kokarin kakaba wa Najeriya kisan kiristoci.
Ya bayyana cewa wani likita ya shaida masa cewa wasu ƙungiyoyin Kiristoci daga yankin Arewa ta Tsakiya ke yin jana’izun ƙarya domin yada labarin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Gumi ya ce bidiyon da ake yada wa a kafafen sada zumunta yana nuna mutane suna binne akwatunan gawa, amma babu kowa a ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gumi ya yi sabon zargi kan kisan kiristoci
Sheikh Gumi ya kara da cewa ana yin hakan ne domin su jawo hankalin duniya da nuna cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi kimar yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargi.
Sheikh Gumi ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:
“Wani likita ya rubuto mini cewa: ‘Shin ka san wasu ƙungiyoyin Kiristoci a yankin Arewa ta Tsakiya yanzu suna birne gawarwakin karya? Suna birne akwatunan gawa babu mutum a ciki suna ɗaukar bidiyo kamar da gaske an kashe mutanem domin su nuna ana kashe Kiristoci. Wannan abin kunya ne."
Malamin ya kara da cewa yana fatan wannan zargi ba gaskiya ba ne, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici idan har ya tabbata.

Kara karanta wannan
Sarkin Musulmi da wasu manyan mutane da Tinubu ya tattauna da su kan barazanar Amurka
Gumi ya karyata kisan kiristoci a Najeriya
Sheikh Gumi ya dade yana musanta zargin cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya bisa dalilai na addini, yana cewa lamarin rikici da ta’addanci ya shafi al’umma baki ɗaya
Wannan furucin na Gumi ya zo ne a daidai lokacin da ake ta cece-kuce a duniya game da rahotannin da ke cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya.

Source: Twitter
Batun kisan kiristocin dai ta samo karfi daga wasu manyan ‘yan majalisar dokokin Amurka suka jagoranta, ciki har da Ted Cruz, Nancy Mace, Riley Moore da wasu.
A watan Oktoba, tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa kiristoci na fuskantar barazana a Najeriya.
Gwamnati ta karyata kisan kiristoci a Najeriya
A baya, mun wallafa cewa Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tattaunawar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka na tafiya cikin fahimtar juna kan zargin kisan kiristoci.
Ministan yada labarai Mohammed Idris ya ce Amurka ta dauki mataki ne bisa bayanan bogi da wasu kungiyoyi ke yadawa, inda ake zargin kisan kiristoci saboda addininsu a kasar nan.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
Amurka ta fara barazanar daukar mataki bayan samun wadannan rahotanni da ta yi imani suna nuna ana tauye hakkin Kiristoci, lamarin da Najeriya ta ce babu shi a kasarta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
