Wasikar da Shugaban INEC Ya Tura Amurka Ta Tada Kura, Kungiyar Musulmi Ta Nemi a Tsige Shi
- Musulman Najeriya sun fara nuna damuwa kan shugaban INEC, Farfesa Amupitan bayan bayyanar wata takarda da ya rubuta
- Farfesa Amupitan ya rubuta takardar tun yana aiki a Jami'ar Jos, ya tura ga shugaban Amurka da Majalisar Dinkin Duniya
- Kungiyar MURIC ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya tsige Amupitan daga shugabancin INEC domin ba zai wa musulmi adalci ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Kungiyar Kare Haƙƙin Musulmi ta Najeriya (MURIC), ta taso shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan.
MURIC ta bankado wata wasika da Farfesa Amupitan ya rubuta, wacce ya alakanra musulmai da kashe-kashen ta'addanci da ke faruwa a Najeriya.

Source: Twitter
Rahoton Daily Trust ta ya nuna cewa MURIC ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tsige Farfesa Amupitan daga kujerar shugaban INEC saboda ra’ayinsa kan batun tsaron kasar nan.

Kara karanta wannan
Shugaban NIWA ya yi murabus daga mukamin da Tinubu ya nada shi, zai nemi takarar gwamna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace wasika shugaban INEC ya tura Amurka?
Tun a lokacin da Amupitan ke aiki a Jami’ar Jos, ya rubuta wata takarda inda ya bayyana cewa, “Ana aikata laifuka a ƙarƙashin dokokin kasa da kasa a Najeriya, musamman laifukan yaƙi, kisan gilla da kisan kiyashi.”
A takardar ya zargi musulmi da kokarin musuluntar da Najeriya, inda ya ce, “
“Kungiyar Boko Haram na da manufar tabbatar da shari’ar Musulunci a Najeriya, yayin da ‘yan bindiga Fulani ke kashe kiristoci don taimaka wa yan uwansu.
Amupitan ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta tilastawa ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana kisan kiyashi su kai ƙarar Najeriya gaban Kotun Duniya (ICJ) saboda gaza magance lamarin.
Ya kuma nemi su turo sojoji su kawo farmaki Najeriya a matsayin mataki na ƙarshe idan lamarin ya gagara, bisa tanadin Sashe na 42 na Kundin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Martanin MURIC ga wannan takarda
A wata sanarwa da shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa:
“Mutumin da ya rubuta wasiƙa mai cike ƙiyayya ga Shugaba Donald Trump yana zargin Musulmai a Arewacin Najeriya, ba za a iya aminta da shi wajen jagorantar zaɓe ba.
Kungiyar ta ce wannan kalamai da Farfesa Amupitan ya taɓa fada sun rusa yardar jama'a a tsarin zaben, musamman ga ‘yan takara Musulmi a Arewa ta Tsakiya da sauran sassan ƙasar.
MURIC ta ce tun bayan bayyanar wannan takarda, “Amupitan ya zama wanda Musulmai ba su aminta da shi a duk wata mu’amala da ta shafi zaɓe ba.”

Source: Twitter
MURIC ta yi kira ga Shugaban Ƙasa
Kungiyar ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sauke Amupitan daga mukaminsa, tare da nada wani sabon shugaban da ya ke da karɓuwa a fadin ƙasa.
MURIC ta ce:
“Muna ba da shawarar a zaɓi wani mutum dabam, wanda ya cancanda ko da addininsa daya da Amupitan, amma a zabi wanda kowane dan kasa zai aminta da shi."
Wani dalibin ilimi, Malam Aliyu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa bai kamata irin wadannan mutanen su hau kujera mai muhimmaci kamar ta shugaban INEC ba.
A cewarsa, idan har ta tabbata shi ya rubuta wannan wasika, to ya bayyana wa duniya karara cewa ba ya kaunar musulmi kwata-kwata, kuma wannan ba abin mamaki ba ne.
Malam Aliyu ya ce:
"Dama Allah ya fada mana a littafinsa mai tsarki cewa ba za su taba kaunar musulmi ba, amma akwai 'yan amana wadanda ake zaman lafiya da su.
"Idan ka duba kalmomin da shugaban INEC ya yi amfani da su a wannan wasika, maganar gaskiya yana cikin wadanda idan suka samu dama ba za su yi wa musulmai adalci ba.
"Ya kamata shugaban kasa ya duba wannan lamari da basira, domin bahaushe na cewa Juma'ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta."
SCSN ta bukaci Tinubu ya sauya Amupitan
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Shari’ar Musulunci ta bukaci Shugaba Tinubu ya sake nazarin nadin Farfesa Joash Amupitan a matsayin shugaban INEC.
Majalisar ta ce akwai rahotanni daga wata gidan jarida da ke zargin Farfesan da rubuta wata takarda a 2020 da ke nuna wariya da ƙiyayya ga Musulmi.
Ta bayyana cewa rubutun ya ƙunshi kalamai masu tada hankali da rashin adalci da suka shafi rikice-rikicen Arewa da jihadin Shehu Ɗan Fodiyo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


