Gwamna Bago Ya Gana da Sojoji, an Lalubo Hanyar Hana 'Yan Bindiga Shiga Neja

Gwamna Bago Ya Gana da Sojoji, an Lalubo Hanyar Hana 'Yan Bindiga Shiga Neja

  • Gwamna Umaru Bago ya kawo wata dabara ta musamman a kan iyakokin Neja don hana shigar ’yan ta’adda daga wasu jihohin Najeriya
  • Bago ya kuma nemi gwamnatin tarayya ta amince a dauki matasa 25,000 daga jihar don taimaka wa sojoji yaki da rashin tsaro
  • Kwamandan dakarun Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Warrah Idris, ya tabbatar da an fara aiki don kawar da ta’addanci a yankin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Neja - Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya bukaci a gaggauta kafa sansanonin sojoji na musamman a kan iyakokin jihar.

Ya bukaci hakan ne domin hana shigowar ’yan ta’adda daga jihohin makwabta da ke addabar jihar da hare-hare.

Gwamna Umaru Bago
Gwamna Umaru Bago da dakarun Operation Fansan Yamma. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Hadimin gwamnan ya wallafa a Facebook cewa Bago ya bayyana haka ne lokacin da kwamandan Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Warrah Idris, ya kai masa ziyara.

Kara karanta wannan

DSS ta tafi kotu da wanda ya nemi a yi wa Tinubu juyin mulki a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a hana 'yan bindiga shiga Neja

Gwamnan ya ce za a kafa sansanonin ne a wuraren da ke da tasiri wajen shiga da fita, musamman a yankunan Mailaka da Kurege da ke karamar hukumar Mariga.

Ya kuma bayyana bukatar gwamnati ta amince da daukar matasa 25,000 daga jihar don taimaka wa sojoji wajen fatattakar ’yan ta’adda da ke addabar al’ummar Neja.

Gwamna Bago ya ce:

“Jiharmu tana da shirye-shirye sosai wajen hada kai da rundunar ku. Muna shirye mu taimaka wajen daukar matasa 25,000 domin su bi diddigin wadannan miyagu.”

Ya ce matsalar rashin tsaro ta hana ci gaban wasu yankuna kamar Kainji da wasu sassan karamar hukumar Borgu, inda ’yan ta’adda suka mayar da wuraren mafaka.

Gwamnan ya bayyana kyakkyawan fatan cewa aikin rundunar Fansan Yamma zai kawo karshen barazanar nan ba da jimawa ba.

Gwamna Bago ya yaba wa sojoji

Gwamnan ya yabawa rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro bisa kokarin da suke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kara karanta wannan

Dambazau: ‘Yan ta’adda sun mamaye garuruwa, suna karɓar haraji da kafa dokoki a Arewa

Gwamna Umaru Bago
Gwamnan Neja, Umaru Bago a wani taro. Hoto: Balogi Ibrahim
Source: Facebook

Ya ce gwamnatin jiharsa tana amfani da wasu hanyoyi wajen samar da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa rundunar Operation Fansan Yamma ta samu cikakken goyon baya da hadin kai.

Martanin Operation Fansan Yamma

A nasa jawabin, kwamandan rundunar, Manjo Janar Warrah Idris, ya bayyana cewa rundunarsa tana da sassa uku karkashinta, ciki har da wani bangare da ke kula da yankunan Jihar Neja.

Ya ce:

“Ziyara ta don sanin wuraren da ke karkashin umarnina ce, don tantance matsalolin tsaro da karfafa gwiwar dakarunmu.
"An ba mu umarni kai tsaye daga babban hafsan tsaro, da kuma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, domin tabbatar da tsaron ’yan Najeriya.”

Ya kara da cewa an fara ayyuka a wuraren Kainji da Babana da sauran yankuna a Borgu, kuma nan ba da jimawa ba za a kammala taswirar ayyuka don daukar matakan da suka dace.

Dalilin kara kai hare hare Kano

A wani labarin, mun kawo muku cewa masana sun yi bayani kan dalilan da suka sanya 'yan ta'adda cigaba da kai hare hare Kano.

Kara karanta wannan

Malamai sun fadawa Tinubu hanyar magance rashin tsaro da zafafan addu'o'i

Masu sharhi kan lamuran tsaro sun bayyana cewa sulhu da ake da 'yan ta'adda a jihohi kamar Katsina na cikin dalilan.

An fara magana kan lamarin ne bayan 'yan ta'adda sun cigaba da zafafa kai hari da sace mutane a wasu yankunan Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng