Matawalle Ya Ga Laifin Wike a kan Musayar Yawu da A.M Yerima
- Karamin Ministan Abuja, Bello Matawalle ya soki Ministan Abuja, Nyesom Wike, bisa sa’insa da jami’in sojan ruwa
- Ya ce bai dace Wike ya rika cacar baki da ƙaramin jami’i ba bayan akwai shugabanninsa da ya dace ya gana da su
- Bello Matawalle ya jinjina wa A.M Yerima bisa ladabi da biyayya da ya nuna a lokacin da Wike ya ja jama'arsa inda sojojin su ke
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Karamin Ministan Tsaro na Tarayya, Dr. Bello Matawalle, ya bayyana cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya tafka kuskure wajen yin sa-in-sa da wani jami’in sojan ruwa.
A ranar Talata ne bidiyon sa'insar Wike da wani jami'in sojan ruwa mai suna A.M Yerima, ya karade kafafen sada zumunta, inda aka hango Wike yana ɗaga murya.

Source: Facebook
Sai dai a wata hira da Matawalle ya yi da DCL Hausa kuma aka wallafa a Facebook, Matawalle ya nuna goyon baya ga matashin jami’in, yana cewa ya nuna ladabi duk da kalaman Wike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya dura kan Wike
A hirar, Matawalle ya ce abin da Wike ya yi bai dace da matsayin sa ba, domin bai kamata ya tsaya yana cacar baki da jami’in da ke bin umarni daga manyansa ba.
A cewar Matawalle, idan akwai wani abu da bai yi daidai ba a wajen aikin, kamata ya yi Wike ya tuntubi manyan Yerima maimakon yin sa’in-sa da shi a bainar jama’a.

Source: Original
Ya ce:
“Bai kamata ma ya yi sa’in-sa da shi ba, saboda akwai shugabannin yaron. Kuma abokin aikinmu ne; idan ma akwai wani abu, mu ya kamata a fuskanta. Kuma wannan yaro abin da ya yi, ya yi ne bisa ka’ida, domin an horar da shi a kan ladabi da biyayya ga doka.”

Kara karanta wannan
Ministan tsaro, Abubakar Badaru ya bai wa A.M Yerima kariya bayan takaddama da Wike
Matawalle ya kara da cewa A.M Yerima ya nuna kwarewa da nutsuwa a lokacin da Wike ke yi masa magana cikin fushi, abin da ya nuna cewa sojan ya san aikin sa.
Ba za a hukunta Yerima ba, cewar Wike
Da yake karin bayani kan yiwuwar hukunta jami’in saboda zargin saba doka, Matawalle ya ce babu wani shirin ladabtar da Yerima.
A cewarsa, jami’in ya yi abin da doka ta tanada kuma ya kiyaye mutuncin rundunar sa yayin da ya ke bin umarni.
Ya ce:
"Ba za a hukunta Yerima ba, saboda bai yi wani laifi ba. Abin da ya yi, ya yi ne bisa ka’ida da horo da ya samu. Ya nuna ladabi, kuma abin yabo ne.”
Matawalle ya kara da cewa duk abin da Wike ya yi wa sojan, kamar ya yi wa Shugaba Bola Tinubu ne saboda shi ne shugaban hafsoshin tsaron Najeriya.
A ƙarshe, Matawalle ya bukaci shugabanni su rika nuna haƙuri da fahimtar juna da jami’an tsaro, domin su ne ginshiƙan kare martabar ƙasa.
Ministan tsaro ya bai wa Yerima kariya
A baya, mun wallafa cewa Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya ce gwamnati za ta kare duk wani jami’in rundunar soji da ke gudanar da aikinsa bisa ƙa’ida da doka.
Jawabin ministan ya zo ne bayan samu rahotannin rikici tsakanin Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da jami’in sojan ruwa, A.M. Yerima, a wani fili a Abuja.
Badaru ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Tsaro ta san da abin da ya faru kuma za ta tabbatar da cewa jami’an da ke gudanar da aikinsu bisa tsari sun samu kariya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

