Gwamnoni Sun Hallara, an Sake Bude Masallacin da Ya Kai Shekaru 217 a Duniya

Gwamnoni Sun Hallara, an Sake Bude Masallacin da Ya Kai Shekaru 217 a Duniya

  • Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara da Gwamna Babagana Zulum na Borno sun halarci taron bude masallacin Juma'a
  • An bude masallacin Imam Gambari da aka gyara a Ilorin wanda ya shafe shekaru fiye da 200 a jihar
  • Masallacin da aka kafa tun 1808, yana daya daga tsofaffin cibiyoyin ilimin addini, yanzu an mayar da shi na zamani

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na Kwara ya jagoranci bude taohon masallacin Juma'a a jihar.

Gwamnan ya halarci bikin tare da takwaransa na Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, domin shaida bude masallacin.

Gwamna ya bude masallacin Juma'a a Kwana
Tsohon masallacin Juma'a da ya kai shekaru 217 da aka bude a Kwara. Hoto: Kwara State Government.
Source: Twitter

Yawan shekarun da masallacin ke da shi

Legit Hausa ta samu wannan sanarwa ne daga shafin gwamnatin jihar wanda ta wallafa a shafin Facebook a yau Laraba 12 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Tinubu, gwamnoni, Sarkin Musulmi za su hadu a Abuja, an gano dalilin haduwarsu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce an bude Masallacin Imam Gambari da aka gyara a Ilorin wanda ya shafe shekaru fiye da 200 a duniya.

Masallacin na da tarihin shekaru 217, kuma yana daga cikin tsofaffin cibiyoyin ilimin addini a Masarautar Ilorin.

An gudanar da taron ne tare da halartar manyan mutane, malamai da shugabannin al’umma daga ciki da wajen jihar.

Gudunmawar da gwamnoni suka bayar a Kwara

Gwamnonin biyu sun bayar da gudummawa don kula da masallacin, yayin da Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya jagoranci bude masallacin tare da kira ga al’umma su ci gaba da ba da tallafi.

Babban Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Solihu, ya gode wa gwamnonin bisa goyon bayansu, inda ya jaddada cewa akwai dangantaka mai karfi ta addini tsakanin Kwara da Borno.

Ya kuma yi addu’a domin zaman lafiya da ci gaba a jihohin biyu da Najeriya baki ɗaya duba da matsalolin tsaro da ake fama da su.

Kara karanta wannan

Minista ya fadawa 'yan Najeriya abin da za su yi bayan barazanar Donald Trump

Shugaban kwamitin gina masallacin, Mai Shari’a Idris Abdullah Haroon (mai ritaya), ya bayyana aikin a matsayin abin nuna hadin kai.

Ya tuna cewa an gina asalin masallacin a 1808 ta hannun dangin Gobir, kuma a 2018 aka fara gyaransa.

An bude tsohon masallaci mai shekaru 217 da aka gyara a Kwara
Taswirar jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Waye ya dauki nauyin kammala aikin masallacin?

Alhaji Yakubu Gobir, wanda shi ne Serikin Gobir da Madawakin Ilorin, ya dauki nauyin kammala aikin gaba daya bayan fuskantar matsin kudi.

Ya ce aikin ibada ne ga Allah wanda al’umma za su mora, ya kuma gode wa Sarki, gwamnati, ma’aikata da masu taimako wajen tabbatar da wannan gagarumin aiki.

Masallacin da aka sake ginawa yanzu yana dauke da dakunan karatu, wuraren ibada na zamani, da kayan aiki na zamani, wanda ke hade tarihi da ci gaba.

Gwamna ya bude manyan masallatai a Sokoto

A baya, kun ji cewa Gwamna Ahmed Aliyu ya kaddamar da sabon masallacin Juma’a da aka gina a Shagari, garin da fitaccen malami Abubakar Gumi ya fito.

Ahmed Aliyu ya ce masallacin alama ce ta ci gaba da kishin addini da al’ada, tare da bukatar al’ummar yankin su kula da ginin dakin ibadan.

Kara karanta wannan

Abubuwa da ya kamata ku sani game da Gwamna Soludo da ya lashe zaben Anambra

Taron ya samu halartar tsohon mataimakin gwamna, Barista Mukhtar Shagari, wanda ya nuna goyon bayansa ga ci gaban addini a Sokoto domin inganta tarbiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.