Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ya Ci Amana, Ya Sace Mota a Gidan Gwamnatin Kano
- Bincike ya fara bankado masu hannu a satar motar ayarin mataimakin gwamna da aka yi a gidan gwamnatin jihar Kano
- Dakarun yan sanda da jami'an wasu hukumomin tsaro sun kama mutum daya da ake zargi kuma sun kwato motar da aka sace
- Bayanai daga ofishin mataimakin gwamnan Kano sun nuna cewa wanda aka kama, direba ne da ke aiki a gidan gwamnatin Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rundunar yan sanda ta matsa kaimi wajen bincike bayan wani barawo ya shiga gidan gwamnatin Kano, kuma ya yi awon gaba da mota.
Rahotanni sun nuna cewa ana zargin wani barawo ne ya sace motar, wacce tana daya daga cikin ayarin motocin mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo.

Source: Facebook
Yan sanda sun kama mutum 1 a Kano
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ’yan sanda sun kama wani mutum da ake zargi da satar motar Toyota Hilux daga cikin jerin motocin mataimakin gwamnan Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ofishin mataimakin gwamnan ya tabbatar da cewa an gano kuma an dawo da motar Hilux ɗin da aka sace.
Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba, ya bayyana cewa rahoton da suka samu daga ’yan sanda ya nuna cewa an bi sawun motar kuma an ƙwato ta da sanyin safiyar Laraba.
An kwato motar gidan gwamnatin Kano
A cewarsa, yan sanda tare da hadin gwiwar wasu jami'an tsaro sun samu nasarar kwato motar ne a wani samame da suka kai wurin da ake zargi.
Yan sanda sun kama mutum daya da ake zargi, kuma an ce mutumin direba ne da ke aiki a gidan gwamnatin Kano.
Bayanai sun nuna cewa direban ya shiga hannu, kuma ya fara taimaka wa yan sanda wajen bincike, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ofishin mataimakin gwamnan ya yaba da ƙwarewar da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suka nuna wajen samun nasarar dawo da motar.
Gwamnatin Kano ta aika sako ga jama'a
Haka kuma, ofishin Abdussalam Gwarzo ya bayyana cewa satar motar wani cin amana ne da wanda ake zargi ya aikata.
A cewar sanarwar:
“Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu, kuma mun kara tabbatar musu da cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne abu mafi muhimmanci a wurin gwamnatin jihar Kano."
Lamarin satar motar da ya ja hankalin mutanen Kano, inda wasu ke ganin gwamnati ta gaza kare gidanta balle kuma talakawa da ke rayuwa a cikin gari.
Rahotanni sun nuna cewa barawon ya samu shiga Fadar ta Gwamnati ta Kofa ta 4, sannan ya fita da motar kusan 5.00 na safiyar Litinin.

Source: Twitter
Gwamnan Kano ya yabawa sojoji
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba wa rundunar sojojin Najeriya da jami’an tsaro bisa matakin da suka dauka cikin gaggawa yayin da yan bindiga suka kai farmaki a Kano.
Gwamma Abba ya ce kokarin da jami'an tsaron suka yi na tunkarar yan bindigan a kan lokaci tare da kashe da dama daga cikinsu abin ya yaba ne.
Ya sanar da bada kyautar motoci sintiri Hilux guda 10 da babura 60 ga rundunar tsaro ta hadin gwiwa da ke aiki a yankunan da abin ya shafa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


