"Ba a Fahimce Shi ba": Shugaban CAN a Arewa Ya Warware Barazanar Trump kan Najeriya
- Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na Arewa, Fasto Joseph Hayab, ya yi tsokaci kan kalaman Donald Trump
- Fasto Hayab ya bayyana cewa an yi kalaman shugaban kasar Amurka gurguwar fahimta kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
- Shugaban na CAN ya bayyana cewa ya kamata a amince cewa ana kai wa Kiristoci hare-hare a wurare da dama a kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na jihohin Arewa 19 da babban birnin tarayya Abuja, Fasto Joseph Hayab, ya yi tsokaci kan barazanar Donald Trump.
Joseph Hayab ya ce an yi wa maganar da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi wa Najeriya kan kashe-kashen Kiristoci, fassara ta kuskure.

Source: Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto Joseph Hayab ya bayyana hakan ne a tattaunawar da aka yi da shi a shirin The Morning Show na gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba, 13 ga watan Nuwamban 2025.
Shugaban CAN ya fayyace maganar Trump
Ya ce Trump bai taba cewa zai kai wa Najeriya hari ba, illa dai ya ja hankalin gwamnatin tarayya ta dauki mataki mai karfi kan ‘yan ta’addan da ke kai wa Kiristoci hare-hare.
“Na saurari abin da Trump ya fada, bai ce zai zo ya yi yaki da Najeriya ba."
“An karkatar da ma’anar abin da ya fada. Abin da ya ce kawai shi ne: ‘Ku bi wadannan ‘yan ta’adda ku kama su; idan ba ku kama su ba, to mu za mu shigo mu kama su.’ To wanene yake tsoron zuwan Trump Najeriya?”
- Fasto Joseph Hayab
Faston ya ce matakin farko wajen samun waraka a kasa shi ne amincewa da gaskiyar cewa ana kai wa Kiristoci hare-hare a wurare da dama.
Hayab ya ba gwamnati shawara
Ya shawarci gwamnati da kada ta raina koke-koken wadanda abin ya shafa, sai dai ta zauna da su, a yi attaunawa ta gaskiya don samo mafita.

Kara karanta wannan
Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya
“Ba za ka gaya wa wanda ya rasa ‘yan uwansa cewa kukansa na karya ne ba. Da zarar mun daina hakan, to mun fara samun mafita. Mu yarda da gaskiyar cewa an zo an kashe Kiristoci, kuma an zo ne da sunan addini."
“Sun zo ne a matsayin masu tsatstsauran ra'ayi. Ba Kiristan da yake cewa Musulmai sun yi taro sun bukaci a zo a kashe su, amma Kiristoci na cewa masu tsatstsauran ra'ayi, 'yan ta'adda sun zo da sunan Musulunci suna kashe Kiristoci."
- Fasto Joseph Hayab

Source: Facebook
Joseph Hayab ya kara da cewa idan an amince da wannan gaskiyar, to hakan ne mataki na farko zuwa ga samun waraka da zaman lafiya.
Ya ce fahimtar juna da jin tausayin juna sune ginshikan dawo da amincewa tsakanin ‘yan kasa.
“Idan muka fara tattaunawa da juna cikin gaskiya, muka fahimci irin zafin da mutane ke ji, mutane za su sake yarda da kowace tattaunawa da gwamnati ke son gudanarwa."
- Fasto Joseph Hayab
Tattaunawar gwamnatin tarayya da Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi tsokaci kan tattaunawar diflomasiyya da take yi da gwamnatin Amurka.
An fara tattaunawa domin inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bayan Amurka ta sako Najeriya a gaba, inda ta fake da batun yi wa kiristoci kisan kare dangi.
Hakan na zuwa ne bayan Amurka ta fara barazanar daukar matakin da ta yi ikirari ne saboda samun bayanai ba daidai ba a kan rashin tsaro a kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

