Ministan Tsaro, Abubakar Badaru Ya Bai wa A.M Yerima Kariya bayan Takaddama da Wike

Ministan Tsaro, Abubakar Badaru Ya Bai wa A.M Yerima Kariya bayan Takaddama da Wike

  • Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta kare duk wani soja da ke gudanar da aikinsa bisa doka
  • Badaru ya yi wannan jawabi ne yayin taron manema labarai kan shirin bikin tunawa da Sojojin Najeriya na 2026 a Abuja
  • Jawabin ya biyo bayan wani rikici a tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da jami’in sojan ruwa, Lt. A.M. Yerima

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ministan Tsaro, Mohammed Badaru, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da kare duk wani jami'in rundunar soji da ke gudanar da aikinsa bisa ka’ida.

Badaru ya bayyana hakan ne a wajen taron manema labarai da aka shirya kan bikin tunawa da Sojojin Najeriya na 2026.

Kara karanta wannan

Hana Wike shiga fili a Abuja, Lauya ya fadi zunubin da sojan ruwa ya aikata

Ministan tsaro Muhammad Abubakar Badaru ya magantu kan rikicin Wike da Yerima
A.M Yerima tare da Ministan tsaro, Muhammadu Badaru Abubakar Hoto: Isa Suleiman Ibrahim/Datti Assalafiy
Source: Facebook

PR Nigeria ta wallafa cewa an shirin gudanar da bikin ne a ranar Laraba a National Defence College, Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta bai wa jami'in soja kariya

TVC News ta wallafa cewa Ma'aikatar tsaron Najeriya ta bayar da tabbatar da cewa gwamnati da rundunar soji za su ci gaba da mutunta jami'ansu.

A cewarsa:

“Za mu ci gaba da kare jami’anmu da ke kan aikin doka."
“Muna bibiyar wannan lamari, kuma ina tabbatar muku cewa duk wani jami’in da ke gudanar da aikinsa bisa doka zai samu cikakken kariya. Ba za mu bari wani abu ya same shi ba muddin yana gudanar da aikinsa yadda ya kamata.”

Minista ya yi jawabi bayan rikicin Wike

Jawabin ministan ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa an samu cece-kuce tsakanin Ministan FCT, Nyesom Wike, da wani jami’in sojan ruwa, Lt. A.M. Yerima.

An samu takaddama ne a kan wani fili da ake cece-kuce a Abuja, wanda ake cewa yana da alaka da tsohon Shugaban Rundunar Sojan Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo mai ritaya.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun taso sojan da ya kalubalanci Wike a gaba, suna neman a kori matashin a aiki

Ministan tsaro ya ce za su kare sojojin Najeriya
Hoton Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar Hoto: Datti Assalifiy
Source: Facebook

Badaru ya ce Ma’aikatar Tsaro ta san da abin da ya faru kuma za ta tabbatar da kare jami’an da ke gudanar da aikinsu bisa doka.

Duk da haka, ministan bai fayyace cikakkun bayanai kan binciken da ake yi ba, amma ya jaddada cewa jami’an da ke kan aikin doka za su samu cikakken kariya.

Lamarin da ya afku a tsakanin Nyesom Wike da A.M Yerima ya ja hankalin mazauna kasar nan, inda ake sharhi a kan dakiyar jami'in sojan.

Wike ya gamu da gamonsa

A baya, mun wallafa cewa An samu rikici a Abuja ranar Talata, 11 ga watan Nuwamba 2005, lokacin da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya je wani fili a Gaduwa.

Wani bidiyo ya bayyana a ranar Talata, inda aka hango Wike yana daga murya a musayar yawu da A.M Yerima, inda ya rika zaginsa da jefansa da maganganu marasa dadi.

Kara karanta wannan

Kalu: Dalilin wasu 'yan majalisa na yunkurin tsige Akpabio daga shugabanci

Hakan ya jawo cece-kuce a tsakanin masu kallo, yayin da ake ta sharhi kan yadda rigingimu irin wannan ke faruwa tsakanin manyan jami’an gwamnati da sojoji a birnin tarayyar Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng