Dalla Dalla: An Ji Abin da Soja Ya Tattauna da CDS a Waya yayin Rigima da Wike

Dalla Dalla: An Ji Abin da Soja Ya Tattauna da CDS a Waya yayin Rigima da Wike

  • An samu bayanai kan tattaunawar waya tsakanin Babban Hafsan Tsaron Najeriya da sojan da ya yi arangama da Nyesom Wike
  • Sojan ya bayyana cewa ‘yan sanda suna barazanar kama ma’aikata a wurin ginin, inda ya ce yana kan aiki bisa umarnin Vice Admiral
  • Hakan ya nuna tashin hankali tsakanin jami’an soja da ‘yan sanda yayin rikicin da ya shafi Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan filin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Bayanai sun sake bayyana kan ainihin abin da sojan da ya yi rigima da Nyesom Wike ya tattauna da hafsan tsaro a Najeriya.

An saki wani muryar tattaunawar waya tsakanin Babban Hafsan Tsaron Najeriya da wani soja mai suna Laftanal Yerima, wanda ya samu sabani da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

An bayanin da soja ya yi a waya da hatsan tsaro
Nyesom Wike da sojan ruwa da suka samu sabani a Abuja. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS | Abuja.
Source: Facebook

Wike: An abin da soja ya tattauna da CDS

Kara karanta wannan

'Yan APC sun taso sojan da ya kalubalanci Wike a gaba, suna neman a kori matashin a aiki

A cikin tattaunawar da mai amfani da X, Imran U Wakili ya wallafa, sojan ya bayyana kansa a matsayin jami’in da ke aiki karkashin Vice Admiral, yana mai cewa yana wurin aikin bisa umarnin manyansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa ‘yan sanda suna barazanar cewa za su doki ma’aikatan idan ba su bar wurin ba, lamarin da ya jawo damuwa a wajen aikin.

Sojan ya ce:

“Barka da safiya ranka ya daɗe, lafiya lau, na gode sosai ranka ya daɗe. Ni jami’i ne karkashin Vice Admiral. Na zo nan bisa umarni.
"Mun tara wasu mutane kaɗan domin su fara aiki a wurin, amma injiniyan wurin yana gaya mana cewa ‘yan sanda suna shirin zuwa su ci mutuncinsu da kuma takurawa ma’aikatan.
"Yan sandan suna barazanar cewa idan ba su bar wurin ba, za su bugesu sannan su kama su. Sun sanar da mu haka, kuma a matsayina na jami’in Vice Admiral, aka kira ni domin in shigo cikin lamarin.
"Ranka ya daɗe, ba mu yin wani abu da ya sabawa doka. Muna nan ne bisa umarnin Vice Admiral.”
An yi rigima tsakanin Wike da sojan ruwa a Abuja
Minista Nyesom Wike yana jawabi bayan rigima da soja a Abuja. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS.
Source: Twitter

Musabbabin rigima tsakanin Wike da soja

Rahoton ya nuna cewa wannan tattaunawar ta kara bayyana irin rashin jituwar da ke tsakanin jami’an sojoji da ‘yan sanda a wurin da rikicin ya faru.

Kara karanta wannan

'Abin da ya kamata a yi wa Wike': Lauya a Kano bayan minista ya kacame da soja

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne daga takaddama kan filin da gwamnati ta rufe wanda sojoji ke cewa yana karkashin umarninsu.

Har yanzu rundunar sojojin ruwa ba ta ce komai ba kan lamarin, duk da cewa jama’a na cigaba da tattaunawa kan wannan sabani a shafukan sada zumunta.

Rahoton ya nuna cewa jami’an tsaro suna cigaba da bincike domin gano musabbabin rikicin da ya hada jami’an soja da ‘yan sanda a Abuja.

Burutai ya gargadi Wike kan rigima da soja

Mun ba ku labarin cewa tsohon hafsan sojan Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya zargi ministan Abuja, Nyesom Wike, da cin zarafin jami’in soja.

Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana lamarin a matsayin barazana ga tsaron ƙasa da kuma tauye martabar dakarun Najeriya.

A bayanin da ya yi, Buratai ya nemi Nyesom Wike da ya nemi afuwa daga shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma jami’in da abin ya shafa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.