Bankin Duniya: Shirin Gwamnatin Tinubu Bai Tabuka Komai Wajen Ragewa Talaka Radadin Fatara ba

Bankin Duniya: Shirin Gwamnatin Tinubu Bai Tabuka Komai Wajen Ragewa Talaka Radadin Fatara ba

  • Bankin Duniya ya ce kasafin da Najeriya ke warewa don walwalar jama’a bai kai na wasu ƙasashen Afrika da ke son inganta rayuwar jama'a ba
  • Sabon rahoton da bankin ya fitar ya kara da cewa wannan ya jawo ba a samu cigaban da ake sa rai ba, musamman ta fuskar rage talauci
  • Rahoton ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na amfani da kashi 0.14 cikin 100 na GDP kawai, alhali wasu ƙasashen Afrika ke ware fiye da haka

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Bankin Duniya ya fitar da wani sabon rahoto da ke nuna cewa kudin da Najeriya ke kashewa a fannin walwalar jama’abai taka kara ya karya ba.

Wannan ya kunshi kudin da ake warewa domin baya da tallafin kayan abinci, taimakon iyalai da shirye-shiryen rage talauci.

Kara karanta wannan

Minista ya fadawa 'yan Najeriya abin da za su yi bayan barazanar Donald Trump

Bankin Duniya ta ce manufar Tinubu ba ta rage talauci ba
Hoton Shugaban Najeriya yayin wani taro a kasar waje Hoto: Ajuri Ngelale
Source: Facebook

BBC Hausa ta wallafa cewa rahoton ya ce ƙasar na amfani da kashi 0.14 cikin 100 na kudin arzikin cikin gida (GDP) a duk shekara domin aiwatar da irin waɗannan shirye-shirye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bankin Duniya ya kwatanta Najeriya da takwarorinta

A cewar bankin, kudin da kasar nan ke warewa bai kai na wasu daga cikin kasashen Afrika ba da ke ware akalla kashi 1.1 domin walwalar jama’a mai karfi.

Bankin Duniya ya bayyana cewa wannan ƙarancin kasafi ya sa ba a ganin wani tasirin a zo a gani da shirin gwamnatin ke yi a rayuwar talaka.

A cikin rahoton, an bayyana cewa talauci a Najeriya ya ragu da kashi 0.4 kacal cikin shekaru masu yawa — abin da ke nuna cewa yawancin jama’a har yanzu suna cikin matsin tattalin arziki.

Bankin Duniya ya shawarci gwamnatin Najeriya

A cewar rahoton, bayanan da Cibiyar Ƙwadago ta Duniya (ILO) ta fitar ya nuna cewa tun daga 2010 zuwa 2021, kasafin Najeriya kan walwalar jama’a bai wuce kashi 0.45 cikin 100 ba.

Kara karanta wannan

Abuja: Wike ya taso masu kadarori a gaba, ya ba su kwanakin biyan tarar N5m

Bankin Duniya ya kwatanta tsarin rage talaucin Najeriya da na sauran kasashen Afrika
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wasu bayanai na 2019 sun nuna cewa idan aka cire bangaren lafiya, adadin kasafin na iya kai kashi 0.7 cikin 100, amma hakan har yanzu bai kai matsakaicin kasafin wasu ƙasashen Afrika ba.

Bankin Duniya ya shawarci gwamnati da ta mayar da hankali wajen gina tsarin walwalar jama’a mai dorewa, domin rage gibin da ke tsakanin masu hannu da marasa shi a ƙasar.

Gwamnati na son rage talauci a Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya na ci gaba da aiwatar da tsarin tallafin kuɗi kai tsaye ga ‘yan ƙasa domin rage zafin babu.

A cewarsa, shirin yana ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɗauka domin tabbatar da cewa talakawa sun ji daɗin sauye-sauyen tattalin arziki da ake aiwatarwa.

Ministan ya jaddada cewa tsarin tallafin yana gudana a bisa tsarin gaskiya, tare da amfani da sabuwar fasaha wajen tabbatar da cewa kuɗin da ake rabawa na zuwa hannun talakawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng