Dalilai 3 da Suka sa 'Yan Bindiga ke Kara Kaimi wajen kai Hari Kano

Dalilai 3 da Suka sa 'Yan Bindiga ke Kara Kaimi wajen kai Hari Kano

  • A kwanakin baya wasu 'yan bindiga sun kai hari a Faruruwa da ke ƙaramar hukumar Shanono, inda suka yi garkuwa da mata biyar ciki har da masu shayarwa
  • Masana sun ce jihar Kano na fuskantar ƙarin hare-hare sakamakon yadda matsin lambar jami’an tsaro a jihohin makwabta ke tilasta wa 'yan bindiga shiga jihar
  • Wani masani a harkar tsaro a Najeriya, Dr Kabiru Adamu ya bayyana abubuwa uku da suka haddasa wannan matsala ta rashin tsaro, ciki har da sauƙin kai hari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace manyan daraktocin ma'aikatar tsaro a kan hanyar zuwa Abuja

Jihar Kano - A farkon wannan mako ne rahotanni suka tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun far wa ƙauyen Faruruwa da ke cikin ƙaramar hukumar Shanono a jihar Kano.

Maharan sun shiga ƙauyen da tsakar dare inda suka yi ta bi gida-gida kafin daga bisani su yi awon gaba da wasu mata biyar ciki har da masu shayarwa.

Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Wani masanin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Security, Dr Kabiru Adamu ya bayyana abubuwa uku da suke jawo kai hari jihar Kano a wata hira da BBC Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Matsin lambar jami’an tsaro a wasu jihohi

Dakta Kabiru Adamu ya bayyana cewa ɗaya daga cikin dalilan da ke haddasa ƙaruwar hare-hare a Kano shi ne matsin lambar jami’an tsaro da 'yan bindiga ke fuskanta a jihohin makwabta.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada belin tsohon Shugaban Faransa Sarkozy, ya fito bayan mako 3 a kurkuku

Ya ce:

“Akwai matakan tsaro masu tsauri da jami’an tsaro ke ɗauka a jihar Katsina, amma babu irin hakan a Kano saboda an ɗauka cewa jihar ba ta da matsalar tsaro sosai.
"Wannan ya sa 'yan bindigar suka karkata zuwa Kano, inda matakan ba su da ƙarfi kamar a Katsina.”

2. Sulhu da 'yan bindiga a Katsina

Adamu ya ƙara da cewa, sulhun da wasu al’ummomi a jihar Katsina suka kulla da 'yan bindiga shi ma yana daga cikin abubuwan da suka sa hare-hare suka ƙaru a Kano.

A cewarsa:

“A iya ƙididdigar da muka yi akwai ƙananan hukumomi 17 a jihar Katsina da suka yi sulhu da 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano da makamai, sun sace mata

"Wannan ya sa hare-hare suka ragu a waɗancan yankunan, amma tun da ba a karɓe makaman 'yan bindigar ba, dole ne su nemi wasu wuraren da za su kai hare-hare.”

Masana tsaro sun sha gargaɗi kan illolin yin sulhu da masu laifi ba tare da an karɓe makaman su ba, domin hakan yana nufin za su ci gaba da aikata ta’addanci a wasu wurare.

3. Sauƙin kai hari a Kano

Dr Adamu ya bayyana cewa, a ilimin kimiyyar tsaro, akwai abubuwa uku da ke sa mai aikata laifi ya ci gaba da kai hari — kasancewar yana kan bakarsa, ribar da zai samu, da kuma sauƙin kai harin.

Ya ce:

“Idan ka duba duka waɗannan abubuwa sun haɗu a Kano. Ga ƙauyuka babu jami’an tsaro, sannan ga riba idan suka kai hare-hare. Wannan shi ne dalilin da ya sa suke ƙara yawaita kai hare-hare a jihar.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mata 9 a Sokoto, sun hallaka wasu

A cewar masanin, sai an ƙara tsaurara matakan tsaro da kafa sansanonin dindindin a yankunan da ke iyaka da Katsina da Kaduna kafin matsalar ta wuce ƙima a jihar Kano.

Hafsun tsaron Najeriya
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Oluyede a ofis. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

An yi gobara a kasuwar Singa a Kano

A wani labarin, mun kawo muku cewa da safiyar ranar Litinin da ta wuce aka tashi da mummunar gobara a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne a kasuwar Singa kuma sama da shaguna 20 ne suka kone.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana wa manema labarai cewa matsalar wutar lantarki ce ta jawo tashin wutar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng