Kalu: Dalilin Wasu 'Yan Majalisa na Yunkurin Tsige Akpabio daga Shugabanci
- Tsohon gwamnan Jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa an yi ƙoƙarin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio
- Ya ce duk da yunkurin tumbuke Akpabio daga kujerarsa ya yi nisa, amma manya sun tsoma baki a lamarin wanda haka ne ya ceci shugaban majalisar
- Kalu ya ce Majalisar Dattawa tana da haɗin kai kuma ba za ta bari rikice-rikicen siyasa su rushe ayyukanta na doka da kulawa da gwamnati ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon gwamnan Jihar Abia kuma sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya tabbatar da cewa labarIN yunƙurin tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Majalisar Tarayya, Abuja, inda ya ce an gano makircin tun kafin ya kai matakin da ba za a iya dakile shi ba.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa a lokacin da aka fuskanci yunkurin wasu daga cikin 'yan majalisar, an yi gaggawar dakile lamarin kafin ya tabbata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya tsira da kujerarsa a majalisa
TVC News ta wallafa cewa Kalu ya ce duk da kokarin da aka yi na tsige Akpabio, amma hadin kansu ya taimaka shugaban majalisar ya tsira da kujerarsa.
Ya bayyana cewa:
“Duk da an yi yunkurin tsige shi, amma ba mu bari hakan ta faru ba. Muna aiki tare a matsayin tsintsiya madaurinki guda, kuma babu rarrabuwar kawuna. Majalisar Dattawa tana da cikakken goyon baya ga shugabancin Akpabio.”
Ya ƙara da cewa manyan ‘yan majalisa suna da niyyar ci gaba da tallafa wa gwamnati domin ceto tattalin arzikin ƙasa.
Kalu ya ce:
“Matsalolin tattalin arziki sun fi komai muhimmanci a gare mu. Dokokin da muke yi suna da nufin taimaka wa Talakawa, domin mu tabbatar kowa yana da abin ci sau uku a rana."
Yadda aka samu baraka a majalisa
Wasu majiyoyi daga cikin Majalisar Dattawa sun bayyana cewa ƙoƙarin tsige Akpabio ya samo asali ne daga wasu ‘yan majalisa da ke jin an ware su wajen raba mukaman kwamitoci.

Source: Facebook
Haka kuma suna ganin shugabancin majalisa ya ware su a bangaren yanke shawara a kan muhimman batutuwa.
Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar jam’iyyar APC da ma na adawa sun yi korafi kan yadda Akpabio ya takaita iko ga ƙungiyar aminansa kaɗan.
Wasu kuma sun nuna rashin jin daɗi a kan yadda ake yanke hukunci a ɓoye, musamman a batutuwan kasafin kuɗi da tsaron ƙasa.
Akpabio da Natasha sun yi cacar baki
A baya, mun wallafa cewa an yi muhawara mai zafi a zaman Majalisar Dattawa tsakanin Godswill Akpabio da Natasha Akpoti Uduaghan a kan kudirin gyaran dokar zubar da ciki a Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, sun yi ka-ce-na-ce kan kudirin.

Kara karanta wannan
Dambazau: ‘Yan ta’adda sun mamaye garuruwa, suna karɓar haraji da kafa dokoki a Arewa
Kudirin na neman ƙara tsaurara hukunci ga duk wanda aka kama da laifin taimakawa ko shirya zubar da ciki a Najeriya, inda ake so a yi wa duk wanda ya yi laifi daurin shekaru 10.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

