Dan Majalisar Wakilai, Sagir Koki Ya Fita daga NNPP, Ya Girgiza Kwankwasiyya

Dan Majalisar Wakilai, Sagir Koki Ya Fita daga NNPP, Ya Girgiza Kwankwasiyya

  • Ɗan majalisar tarayya daga Kano Municipal, Sagir Ibrahim Koki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP
  • A sanarwar da ya fitar, ya danganta matakinsa da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar a matakin ƙasa
  • Hon. Sagir Ibrahim Koki ya ce rikicin ya hana shi aiwatar da wakilci nagari ga al’ummar yankinsa da suka zabe shi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Dan majalisar wakilai daga Kano Municipal, Sagir Ibrahim Koki, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP.

Ya fita daga NNPP ne bisa dalilin rikicin cikin gida da ke ci gaba da raba kawunan shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Sagir Ibrahim Koki
Dan majalisar wakilai, Sagir Ibrahim Koki. Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Hon. Koki ya yi ne a wani sako da Imram Muhammad ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sanata PDP ya jefar da jam'iyya mai adawa, ya fadi amfanin da APC za ta yi masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta samun ƙarin ‘yan siyasa daga Kano da ke barin jam’iyyar NNPP, musamman sakamakon rashin jituwa da ke kara kamari.

A wasikar da ya aike wa shugabar mazabarsa ta Zaitawa a karamar hukumar Kano Municipal a ranar 11, Nuwamba, 2025, Koki ya bayyana cewa ficewarsa na bisa ‘yancinsa a tsarin mulki.

Dalilan ficewar Hon. Koki daga NNPP

A cikin wasikar, ɗan majalisar ya bayyana cewa rikicin shugabanci a jam’iyyar NNPP ya haifar da matsaloli masu tsanani da suka hana shi gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Ya ce:

“Saboda rikicin cikin gida da ya dabaibaye shugabancin jam’iyyar NNPP, ya zama da wuya ko ma ba zai yiwu ba in ci gaba da wakiltar mutanen Kano Municipal yadda ya dace.”

Hon. Koki ya yi nuni da cewa ya yanke wannan shawara ne domin kare mutuncinsa da kuma tabbatar da cewa al’ummar da yake wakilta ba su rasa wakilci mai inganci a majalisa.

Kara karanta wannan

NNPP ta zargi Kwankwaso da cin amanar jam'iyya, an ambaci laifuffukansa

Hon. Koki ya dogara da tsarin mulki

A cewar wasikar da ya rubuta, Koki ya jingina ficewarsa da sashen 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Rabiu Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf na NNPP a Kano. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Ya kuma dogara da sashe na 7.1 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar NNPP, wanda ke ba kowane ɗan jam’iyya ‘yancin fita idan ya ga dacewa.

Daily Trust ta a rubuta cewa ya ce:

“Da yardar sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya da sauran dokoki masu alaƙa da haka, ina sanar da ficewa ta daga jam’iyyar NNPP daga yau, Talata, 11, Nuwamba, 2025.”

Hon. Koki ya gode wa jam’iyyar NNPP

Duk da ficewar tasa, Koki ya nuna godiya ga jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a karkashinta a zaben 2023, wanda ya samu nasara.

Ya ce:

“Ina godiya ƙwarai da gaske ga jam’iyyar bisa damar da ta bani don yin takara a karkashin tutarta.
"Goyon baya da amincewa da nake samu daga ‘ya’yan jam’iyyar sun kasance masu muhimmanci gare ni, kuma zan ci gaba da jin daɗin wannan haɗin kai.”

Kara karanta wannan

Dambazau: ‘Yan ta’adda sun mamaye garuruwa, suna karɓar haraji da kafa dokoki a Arewa

Hon. Kofa ya koma APC daga NNPP

A wani labarin, mun kawo muku cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji a Kano ya koma APC.

Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya sauya sheka ne bayan jam'iyyar NNPP ta sanar da korar shi wata biyu da suka wuce.

Kofa ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin marawa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027 mai zuwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng