Gwamnatin Najeriya Za Ta Kera Makaman Yaki da Kanta, An Kulla Sabuwar Yarjejeniya
- Ma’aikatun karafa da tsaro sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fara kera makaman yakin soji a kamfanin karafa na Ajaokuta
- Yarjejeniyar ta hada da kera motoci masu sulke, makamai, kwalkwali da kayan tsaro don kara karfin harkokin tsaro a Najeriya
- Ministan karafa, Abubakar Audu da ministan tsaro, Bello Matawalle sun ce shirin zai farfado da masana’antu da tattalin arziki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta dauki sabon mataki na bunkasa masana’antu da tsaro bayan rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin ma’aikatar bunkasa karafa da ta tsaro.
Wannan yarjejeniyar, za ta taimaka wajen samar da makamai, motocin yaki, da duk wasu kayayyaki da sojojojin Najeriya ke amfani da su.

Source: Twitter
An rattaba hannun ne a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, a hedikwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja, karkashin jagorancin ministan karafa, Prince Abubakar Audu, da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, in ji rahoton Punch.

Kara karanta wannan
Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yarjejeniyar kera makamai a Najeriya
Sanarwar da ma’aikatar karafa ta fitar ranar Talata ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta bai wa kamfanin sarrafa karafa na Ajaokuta damar kera motoci masu sulke, makamai, kwalkwali da sauran kayan tsaro tare da hadin gwiwar hukumar DICON.
Ministan karafa, Prince Abubakar Audu, ya bayyana wannan mataki a matsayin “sabuwar hanya ta tabbatar da cin gashin kai a harkar tsaro da raya masana’antu.”
“Ajaokuta ita ce daya daga cikin manyan kadarorin masana’antu a Afirka. Wannan yarjejeniya ta nuna jajircewarmu wajen amfani da karfin kamfanin domin bunkasa tsaro da tattalin arziki."
- Prince Abubakar Audu.
Ya ce shirin zai taimaka wajen kawo ayyukan yi, rage dogaro da shigo da makamai daga kasashen waje, da kuma bunkasa kirkire-kirkiren cikin gida, in ji rahoton Channels TV.
Matawalle da DICON sun yaba
A nasa bangare, karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce yarjejeniyar na zuwa ne a lokaci da Najeriya ke neman ingantaccen mafita ga matsalolin tsaro da tattalin arziki.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
Matawalle ya ce:
“Wannan yarjejeniya tana da mahimmanci saboda ta hada tsaro da ci gaban tattalin arziki a lokaci guda."
Haka kuma, Daraktan DICON, Manjo Janar Ibrahim Babatunde Alaya, ya ce wannan mataki zai samar da ayyukan yi, gina kwarewar cikin gida, da rage dogaro da kayayyakin tsaro daga waje

Source: UGC
Farfado da Ajaokuta da manufar Tinubu
Kamfanin karafa na Ajaokutawanda aka kafa a shekarun 1970 domin zama ginshikin masana’antun Najeriya, ya dade yana fama da rashin kulawa da gazawar aiki.
Sai dai gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakin sake farfado da kamfanin ta hanyar hadin gwiwa da hukumomi daban-daban.
Ana ganin wannan yarjejeniya a matsayin sabuwar hanya ta inganta masana’antu da tsaro, tare da mayar da hankali kan amfani da albarkatun cikin gida da sauyin fasaha.
An fara kera makamai a Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, IGP Kayode Egbetokun ya kai ziyarar gani da ido kan wasu kayayyakin tsaro da masana fasaha na cikin gida suka kirkira a Abuja.

Kara karanta wannan
Sokoto: Gwamnati ta musanta sakaci kan harin 'yan bindiga, ta bayya yadda lamarin yake
A yayin ziyarar, an gabatar da wasu sababbin fasahohin leken asiri, jiragen yaki marasa matuka, da sauran na’urorin zamani da aka kirkira a gida.
Babban sufetan 'yan sandan ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda na da niyyar hada gwiwa da kamfanonin fasaha na cikin gida domin bunkasa hanyoyin yaki da laifuffuka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng