Yan Bindiga Sun Sace Manyan Daraktocin Ma’aikatar Tsaro a kan Hanyar Zuwa Abuja
- ‘Yan bindiga sun kai farmaki kan wasu manyan daraktoci da ke kan hanyarsu ta zuwa Abuja daga jihar Lagos
- Maharan sun sace daraktoci shida na ma’aikatar tsaron ƙasa yayin da suke tafiya daga Lagos zuwa Abuja domin jarabawa
- Ƙungiyar ASCSN ta tabbatar da sace mutanen tare da bayyana sunayen waɗanda abin ya shafa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wasu manyan daraktoci da suke kan hanyarsu ta zuwa Abuja a jihar Kogi.
Yan bindigar sun sace daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaron Ƙasa yayin da suke kan hanyar zuwa Abuja domin shiga jarabawar karin matsayi a matakin daraktoci.

Source: Facebook
An sace daraktocin ma'aikatar tsaro
Rahoton Tribune ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin 10 ga watan Nuwambar 2025 da muke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maharan sun sace mutanen ne a hanyar Kabba-Lokoja-Abuja, inda aka ce an yi musu kwanton ɓauna.
Wannan lamarin ya girgiza Ma’aikatar Tsaro da ƙungiyar manyan ma'aikata a Najeriya (ASCSN), inda aka fara bayyana damuwa kan tsaron ma’aikata masu yin dogon tafiya don ayyukan gwamnati.
A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Shehu Mohammed, da sakataren janar, Joshua Apebo, suka fitar, ƙungiyar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana ƙoƙarin ganin an ceto waɗanda aka sace.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda aka sace sun haɗa da: Mrs. Ngozi Ibeziakor, Mrs. C.A. Emeribe, Mrs. C. Helen Ezeakor, Mrs. C.A. Ladoye, Mrs. J.A. Onwuzurike da Mrs. Catherine O. Essien dukkansu ma’aikata ne a 'Command Day Secondary School' (CDSS), Ojo da ke Lagos.

Source: Original
An tura jami'an tsaro domin kubutar da su
Ƙungiyar ta bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro ta tura jami’an tsaro domin tabbatar da kubutar da waɗanda aka sace cikin koshin lafiya, Punch ta ruwaito.
“Mun dade muna shawartar Hukumar Kula da Ma’aikatan Tarayya da ta rika gudanar da jarabawar matsayi a jihohi, maimakon tilasta ma’aikata su yi dogon tafiya zuwa Abuja."
- Cewar ƙungiyar.
ASCSN ta kuma gargadi gwamnati kan hatsarin da ma’aikata ke fuskanta saboda tsananin rashin tsaro da mummunan yanayin hanyoyi.
Ta ce:
“Idan ba a dauki mataki ba, irin waɗannan abubuwan na iya ƙaruwa.”
A halin yanzu, Ma’aikatar Tsaro ta fara bincike tare da tura tawagar jami’an tsaro na musamman domin gano inda aka boye waɗanda aka sace a jihar Kogi.
Ƙungiyar ASCSN ta yaba da saurin daukar matakin ma’aikatar, tana kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar sun ceto daraktocin ba tare da wata matsala ba.
Yan bindiga sun bude wuta kan matafiya
Kun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun jefa jama'a a cikin tashin hankali bayan sun tare wadansu ma’aikatan INEC a jihar Kogi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa mayakan dauke da makamai sun sace mata uku daga cikin matafiya a hanyarsu ta zuwa jihar Anambra.
Sun nufi jihar Anambra ne domin gudanar da zabe, sai dai yan ta'addan sun tare su a iyakar jihohin Kogi da Benue.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

