Hotunan Abba Kabir da Ganduje Sun Yi Kicibis a Karon Farko tun bayan Zaben 2023
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje sun hadu a jihar Kano
- Ganduje da Abba Kabir sun hadu ne a karon farko tun bayan zaben da aka gudanar na shekarar 2023 da ya gabata
- Haduwar ta faru ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda suka gaisa cikin natsuwa da yanayi na nuna girmamawa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, sun hadu karo na farko tun bayan zaben 2023.
An ruwaito cewa haduwar ta faru ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda suka yi musayar gaisuwa cikin natsuwa da farin ciki a fuskokinsu.

Source: Facebook
Ganduje ya yi kicibis da Abba Kabir
Legit Hausa ta samu wani bidiyo da shafin Gandujiyya Online ta wallafa a shafin Facebook a yau Talata 11 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ne karo na farko da suke ganin juna a fili tun bayan tazarar shekara biyu da kuma zaben da ya kasance cike da kalubale wanda ya kai ga zuwa kotu.
Rahotanni sun bayyana cewa haduwar ta kasance ta bazata, inda suka yi gaisuwa cikin yanayi na abokantaka da mutunta juna sosai.

Source: Facebook
Yadda Abba Kabir ya hadu da Ganduje
Ganduje wanda yanzu shi ne shugaban hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa, FAAN, ya je Kano don duba aikin filin jirgi.
A gefe guda kuma, Gwamna Yusuf yana kan hanyarsa zuwa Abuja don halartar wata ganawa, kafin suka hadu a wurin filin jirgin.
An ce tsohon gwamnan ya samu tarba daga manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, yayin da Yusuf ya samu rakiyar wasu manyan jami’an gwamnati.
Ganduje bai halarci mikawa Abba mulki ba
A lokacin mika mulki bayan zaben 2023, Ganduje bai halarta ba, sai ya tura sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji domin shaida rantsuwar Abba Kabir Yusuf.
A lokacin zaben, Gwamna Yusuf na jam’iyyar NNPP ya doke dan takarar APC Nasiru Yusuf Gawuna, wanda Ganduje ya goyi bayansa da dukan karfinsa.
Daga bisani, Nasiru Gawuna da jam'iyyarsa sun garzaya kotu domin neman yi musu adalci kan abin da suka kira magudi kafin daga karshe, kotu ta ba Abba Kabir nasara.
Wannan ganawa ta farko bayan shekaru biyu na siyasar gaba ta nuna alamun mutuntaka da fara’a tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar Kano.
Ganduje ya soki gwamnatin Abba Kabir
An ji cewa tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi maganganu masu kaushi kan gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da gwamnatinsa a jihar.
Ganduje ya yi zargin cewa gwamnatin Gwamna Abba ba ta da masaniya kan harkokin mulki kuma tana kashe kudade kan ayyukan da ba su dace ba wanda hakan ke jawo koma baya ga Kano.
Tsohon shugaban na jam'iyyar APC mai mulki, ya kuma bayyana cewa kudaden da Gwamna Abba ya samu cikin watanni shida, bai same su cikin shekaru takwas ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

