Wike Ya Gamu da Gamonsa, Soja Ya Ki Bari Ya Tozarta Shi a bainar Jama'a

Wike Ya Gamu da Gamonsa, Soja Ya Ki Bari Ya Tozarta Shi a bainar Jama'a

  • An samu tashin hankali a Abuja yayin da sojoji suka hana Ministan Abuja, Nyesom Wike, shiga wani fili da ake rikici a Gaduwa
  • Wike ya yi fada da sojojin da suka ce suna bin umarni daga sama, yayin da ya zarge su da amfani da iko wajen zaluntar jama’a
  • Ministan ya bayyana takaicinsa, yana cewa tsohon hafsan sojan ruwa bai kamata ya yi amfani da mukaminsa wajen karɓar fili ba bisa ka’ida ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An samu rikici a Abuja lokacin da sojoji suka hana Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, shiga wani fili da ke Gaduwa.

Nyesom Wike ya je wurin ne tare da jami’an hukumar raya babban birnin tarayya, FCDA, amma sojojin da ke wurin suka hana su shiga.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada sabon ministan jin kai ana cikin neman a biya kudin N Power

Wike ya yi cacar baki da soja a Abuja
Nyesom Wike da dakarun sojoji a Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Twitter

Abin da ya fusata Wike a birnin Abuja

Hakan na cikin wani faifan bidiyo da Iniobong Udoh ya wallafa a Facebook a yau Talata 11 ga watan Nuwambar 2005 inda aka gano sojan na sa'insa da Nyesom Wike.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya fusata sosai, yana daga murya yana tambayar dalilin da yasa aka mamaye filin saboda tsohon hafsan rundunar sojan ruwa ne ya mallaki wurin.

“Saboda shi tsohon hafsan sojojin ruwa ne ya karɓi fili babu ka'ida?"

- Cewar Nyesom Wike cikin fushi

Sai jami’in sojan ya mayar da martani yana cewa an mallaki filin bisa doka, yana mai cewa:

“Ni soja ne mai gaskiya."

Bisa ga dukkan alamu martanin sojan ya batawa Wike rai inda ya fusata nan take tare da tsawatarwa sojan.

“Ka yi shiru!” Wike ya tsawata masa, amma jami’in ya amsa da cewa, “Ba zan yi shiru ba.”

Wike ya kara da cewa:

"Kai babban wawa ne. Lokacin da na kammala makaranta kai kana firamare. Za mu gani ko za ka ci gaba.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Matasa sun bankawa shingen binciken hukumar 'Immigration' wuta

An samu rigima tsakanin Wike da wani soja a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike a yayin taro a Abuja. Hoto: Nyesom Wike.
Source: Facebook

Yadda masu tsaron Wike suka lallashi sojoji

Jami’an tsaron da ke tare da Nyesom Wike sun yi ƙoƙarin lallashin sojojin su bar shi ya shiga, amma sun nace suna cewa suna bin umarni daga sama.

Wike ya yi Allah-wadai da abin da ya kira rashin mutunci, yana cewa ba za a bar mutane su rika amfani da bindiga su tsoratar da gwamnati ba, cewar Daily Trust.

Ya ce ba zai taɓa bari a yi amfani da mukami ko karfi wajen tauye hakkin jama’a ba, yana cewa:

“Ba zan taɓa yarda da barazana ba.”

Wike ya taso masu kadarori a gaba

A baya, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bai wa masu gine-ginen da suka karya dokokin amfani da ƙasa wa'adin ceto kadarorinsu.

Ministan ya shaida cewa har yanzu suna da damar gyara kuskuren da suka tafka idan suka biya rarar N5m a cikin kwanaki 14 masu zuwa.

Kara karanta wannan

Abuja: Wike ya taso masu kadarori a gaba, ya ba su kwanakin biyan tarar N5m

Wike ya ce waɗanda suka gaza biyan kudin a cikin wadannan kwanaki 14, za a ɗauki matakan tilasta masu bin dokar da aka tanada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.