"Ba Karya Ba Ne": Sanata Kalu Ya Goyi bayan Kalaman Trump kan Najeriya
- Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa ya yi magana kan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi wa Najeriya
- Uzor Orji Kalu ya bayyana goyon bayansa kan kalaman da Trump ya yi dangane da kashe-kashen da ake yi a kasar nan
- Sanatan ya nuna cewa ko kadan babu karya a kalaman Trump, domin ana kashe Musulmai da Kiristoci a Najeriya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar ci gaban yankin Kudu maso Gabas (SEDC), Sanata Orji Uzor Kalu ya goyi bayan shugaban Amurka, Donald Trump.
Sanata Uzor Kalu ya goyi bayan Trump ne kan kalamansa game da kashe-kashen da ake yi a Najeriya, yana mai cewa ya fadi gaskiya.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa Sanata Kalu ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jarida a ranar Talata, 11 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Kalu ya ce kan kalaman Trump?
Sanata Kalu ya ce hare-haren da ake yi a kasar nan sun shafi Kiristoci da Musulmai baki ɗaya, kuma dole ne a dauki mataki mai tsanani a kansu.
“Idan za a ce karya ne, to amsar ita ce ba karya ba ne saboda ya fadi gaskiya. Ana kashe ’yan Najeriya, ko Kiristoci ne, ko Musulmai."
"Akwai ’yan jihadi da ke son su rusa Najeriya gaba daya. Dole mu sanya su a jerin masu laifi ba tare da tausayawa ba domin a kamo su daga maboyarsu.”
Sanata Kalu ya bayyana cewa ya taba tattaunawa da tsofaffin shugabannin Amurka biyu, daya dan jam’iyyar Republican, daya kuma dan Democrat, da kuma Sanatoci shida, wadanda dukkansu sun nuna shirin taimaka wa Najeriya wajen yakar ta’addanci.
“Kafin Shugaba Trump ya fadi maganar, hukumar leken asirin Amurka ta riga ta gano inda wadannan ’yan ta’adda suke."
“Kuna ganin dakarun sojoji saman Najeriya har sun fara aiki, mai yiwuwa ne suna amfani da bayanan da Amurka ta raba musu wajen kai hare-hare kan maboyar ’yan ta’adda. Haka ya kamata a yi.”

Kara karanta wannan
'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata
- Sanata Uzor Orji Kalu
Kalu ya koka kan rikice-rikice
Sanata Kalu wanda ya ce rikice-rikicen duniya da dama sun samo asali ne daga harin da Amurka ta kai da kashe shugabannin Libiya, Muammar Gaddafi, da na Iraki, Saddam Hussein.
Ya ce wadannan kashe-kashen sun haddasa yaduwar makamai a fadin Afirka.
“Lokacin da aka kashe Gaddafi da Saddam Hussein, matsala ta taso. Wadannan mutanen suna rike da iyakokinsu da tsaro."
"Bayan mutuwarsu, makamai sun yadu a duniya, kuma yanzu mu ne muke fama da sakamakon hakan.”
- Sanata Uzor Orji Kalu

Source: Facebook
Sanatan ya kuma karyata jita-jitar cewa Amurka na niyyar ruguza gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa wadanda Amurka ke nufin kai wa hari su ne ’yan jihadi da ke lalata Najeriya, ba gwamnati ba.
“’Yan Najeriya suna tafi, wasu kuma suna tunanin Amurka tana shirin ruguza gwamnatin Tinubu. A’a! Ba haka ba ne. Amurka za ta kai farmaki ne kan ’yan jihadi."
- Sanata Uzor Orji Kalu
Najeriya ta fara tattaunawa da Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara tattaunawa da gwamnatin Amurka kan zargin kisan Kiristoci.
Gwamnatin Najeriya ta fara zaman tattaunawa da gwamnatin Amurka domin fayyace gaskiya da warware sabanin fahimtar da aka samu.
Tattaunawar dai na taimakawa wajen fayyace wasu kurakurai da rashin fahimta game da halin tsaron da Najeriya ke ciki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

