'Yan Sanda Sun Tarwatsa Yunkurin Sace Jami'ansu da Limamin Addini a Abuja
- Rundunar 'yan sanda da ke Babban Birnin Tarayya ta tarwatsa yunƙurin satar ma’auratan jami’ansu da wani limamin coci a Abuja
- Wadanda ake zargi da kai harin sun tsira da kyar bayan an yi artabu da musayar wutar da ta jikkata su a bata-garin mutanen
- Ana ci gaba da sintiri tare da hadin gwiwar masu gadi, farar hula, da sauran jami’an tsaro don kama wadanda suka tsere
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Rundunar ‘yan sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta tarwatsa yunƙurin satar jami’an ‘yan sanda biyu da wani Fasto a Abuja.
Jami’an da abin ya shafa sun hada da DSP Gabriel Tanko, dake aiki a Sashen Bincike na Rundunar ‘Yan Sanda, da matarsa, Jummai Tanko, wadda ke aiki a Hedkwatar Zone 7.

Source: Facebook
Wasu majiyoyi sun tabbatar wa Zagazola Makama cewa an kai hari ne a gidansu dake Aco Phase 2, kan titin GAU, da safe a ranar Litinin, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kai wa 'yan sanda hari
Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru tsakanin karfe 12.00 na tsakar dare zuwa 1.30 na safe a ranar 10 ga Nuwamba, bayan rahoton sirri ya nuna cewa kungiyar ta shirya sace ma’auratan.
Shugaban Rundunar Yaki da Sata ta jagoranci tawaga don kamo masu laifin a wani wurin tsaunuka kusa da gidan da aka kai hari.

Source: Facebook
Majiyar ta ce:
“A kimanin 1.02 na safe, ‘yan fashi da makami da yawa sun kusanci gidan,an yi musayar wuta na tsawon minti 15, inda jami’an suka tilasta wa masu laifin tserewa, wasu daga cikinsu da raunuka."
Jami'an sun samu nasarar ceto ma’auratan, yayin da mazauna unguwar da suka firgita saboda musayar wuta da aka dade ana yi.

Kara karanta wannan
Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji
Ana bibiyar 'yan ta'adda a Abuja
Rundunar ‘yan sanda ta kara tsaro a gidan wani Fasto a kusa da cocin ECWA a wannan yankin, wanda ake zargin shi ma na cikin wadanda za a mai wa hari.
Ana gudanar da sintiri tare da hadin gwiwar masu gadi, farar hula masu kulawa, da sauran jami’an tsaro.
Hakanan an umarci mazauna yankin da cibiyoyin lafiya da su kai rahoto idan suka ga wani da ke da raunukan harsashi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Rundunar ta bayyana cewa ana ci gaba da kokarin bin sawun wadanda suka tsere, don tabbatar da cewa an kama duk masu hannu a wannan yunƙurin satar.
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane
A baya, mun wallafa cewa rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Delta ta tabbatar da cafke mutum mai shekaru 60 da wasu biyu bisa zargin yin garkuwa da mutane tare da karɓar kudin fansa.
A cewarsa, bayan samun rahoton garkuwa da mutane biyu a ranar 3 ga Oktoba a Asaba, rundunar ta tura jami’an yaki da garkuwa da mutane da laifuffukan yanar gizo domin bincike.
Binciken ya kai ga cafke Ndianefo Cypre, mai shekaru 60, wanda aka gano cewa asusun bankinsa ne aka yi amfani da shi wajen karɓar kudin fansa bayan an cafke mutane.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

