Rai Ya Yi Halinsa: Mahaifiyar Minista a Gwamnatin Tinubu Ta Rasu
- An shiga jimami a Najeriya bayan sanar da rasuwar mahaifiyar minista a gwamnatin Bola Tinubu a jihar Kaduna
- An tabbatar da cewa ministan Muhalli, Malam Balarabe Lawal, ya rasa mahaifiyarsa, Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu
- Majiyoyi sun ce dattijuwar ta rasu a Zaria da ke jihar Kaduna a yammacin Lahadi bayan fama da rashin lafiya mai tsawo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Ministan Muhalli a Najeriya, Malam Balarabe Abbas Lawal, ya shiga cikin jimami bayan rasuwar mahaifiyarsa.
An tabbatar da cewa marigayiyar, Hajiya Dayyabatu Lawal Aliyu, ta rasu a garin Zaria, jihar Kaduna bayan fama da jinya.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar mahaifiyar minista a Najeriya
Hakan na cikin wata sanarwa da ma'aikatar muhalli a Najeriya ta wallafa a shafinta na yanar gizo a ranar Lahadi 9 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar, Ibrahim Haruna shi ya tabbatar da haka a sanarwar da ya sanyawa hannu.
Haruna ya yi addu'a ga marigayiyar domin neman Ubangiji ya yi mata rahama da kuma sanya ta gidan aljanna Firdausi.
Sanarwar ta ce:
"Sallar jana’iza za ta gudana a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, da ƙarfe 11:00 na safe, a Bambale, cikin garin Zaria.
"Allah Madaukakin Sarki ya gafarta mata kura-kuranta, ya ba ta Aljannatul Firdaus, ya lullube ta da rahamarsa marar iyaka, ya kuma ba iyalanta haƙuri da juriyar wannan babban rashi. Amin.

Source: Original
Yaushe aka yi jana'izar marigayiyar a Zaria
Majiyoyi sun tabbatar da cewa tuni aka yi sallar jana'izar marigayiyar a jiya Litinin 10 ga watan Nuwambar 2025 a birnin Zaria da ke jihar Kaduna.
Wani majiya daga dangin marigayiyar ya shaida cewa ta rasu ne da yammacin Lahadi 9 ga watan Nuwambar 2025 bayan jinya mai tsawo a gidanta.
An bayyana cewa marigayiya Hajiya Dayyabatu ta rasu tana da shekaru 93 a duniya, ta bar ‘ya’ya hudu da jikoki masu yawa.
Kwamishina a Kaduna ta yi ta'aziyya
Kwamishinar mata a jihar Kaduna ta tura sakon ta'aziyya ga ministan kan rashin da ya yi na mahaifiya wanda ya rasu a yammacin ranar Lahadi 9 ga watan Nuwambar 2025.
Rabi Salisu ta nuna jimaminta kan rashin dattijuwar inda ta yi addu'ar Ubangiji ya yi mata rahama da kuma sanya ta gidan aljanna firsausi.
Kwamishinar ta bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ta yi a shafin Facebook a jiya Litinin 10 ga watan Nuwambar 2025.
Mahaifiyar Adamu Mu'azu ta bar duniya
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Bauchi, Ahmad Adamu Mu’azu, ya yi rashin mahaifiyarsa bayan ta sha fama da jinya inda al'umma suka yi mata addu'o'i.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana jimaminsa, yana cewa marigayiyar ta yi rayuwa ta ibada, zumunci da son jama’a.
Gwamnan ya mika ta’aziyya ga iyalan Adamu Mu’azu, yana addu’ar Allah ya gafarta mata ya kai ta Aljanna Firdausi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
