INEC: Ana So Tinubu Ya Sauke Amupitan bayan Gano 'Ƙagen' da Ya Yi wa Musulmin Arewa

INEC: Ana So Tinubu Ya Sauke Amupitan bayan Gano 'Ƙagen' da Ya Yi wa Musulmin Arewa

  • Tsohon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Aliyu U. Tilde ya bukaci Shugaban INEC, Joash Amupitan ya sauka daga mukaminsa
  • Tilde ya zargi shugaban hukumar da nuna bambanci tsakanin addinai da kabilu a kan batun da ya ce sharri ne kawai aka yi
  • Tun bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sako Najeriya a gaba aka rika fito da rubutun Amupitan a kan zargin kisan kiristoci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Aliyu U. Tilde, tsohon kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, ya yi kira ga Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ya sauka daga mukaminsa.

Dr. Tilde ya zargi Amupitan da yin rubutun karya tare da nuna nuna bambanci ga wasu kabilu da addinai a kasar nan.

Kara karanta wannan

Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu

Shugaban INEC Amupitan zai fuskanci matsala
Shugaban kasa, Bola Tinubu tare da shugaban INEC, Amupitan Hoto: X/@aonanuga1956
Source: Twitter

Aliyu U. Tilde ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya zargi tsohon malamin na sa da yada labaran karya a kan Musulmin Arewa.

Amupitan ya fusata jama'a

A wani rubutu da ya yi a kafar sada zumunta, Tilde ya ce rubutun Amupitan a kan zargin Musulmi da yi wa kiristoci kisan kare dangi, abin kunya ne matuka.

Ya ce:

“Wannan abin kunya ne kuma rashin gaskiya ga mukaminsa. Ya yi karya kan Kiristoci, Musulmai, Hausawa da Fulani ba tare da hujja ba. Abin kunya ga malaminmu da ya san dioka!"
"Nazarin takardunsa ya nuna cike yake da kura-kurai. Ina jin kunya cewa wannan ya fito daga malamina a 2003. Bayani zai zo gobe, in sha Allah.”

Dan jarida ya soki Amupitan

Baya ga Tilde, wani fitaccen 'dan jarida a Kano, Nasiru Salisu Zango ya yi zargin cewa Amupitan makiyin Fulani da Musulmai ne, saboda haka ya ajiye aiki.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Ana zargin Amupitan da nuna kiyayya ga Musulmi
Hoton Shugaban INEC na kasa, Amupitan Hoto: @Tokunboabiru
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Zango ya ce:

"Wasikar Amupitan ta nuna kiyayyar sa ga musulmi da fulani ya kamata ya sauka daga shugabancin INEC."

Wannan lamari ya jawo ra'ayoyi daban-daban a sahar, inda wasu ke ganin cewa babu laifi a kalaman da Amupitan ya yi amfani da su a baya.

Hadimin Atiku Abubakar, AbdulRasheeth Shehu ya bayyana goyon bayansa ga Tilde, inda ya ce:

“Tinubu ma a baya yace bai yadda da Najeriya daya ba, yau shine shugaban kasa. Abubuwan kasar nan sai Allah ya tsara. Amma babu abin da zai canja.”

Sani Abdullahi Muaz ya bayyana cewa:

“Bana goyan bayan a sauke shi saboda kafin shugaban kasa ya dora shi sai da ya yi shawara da duka gwamnoninmu sannan suka ce sun yarda. Ba a same shi da wani laifi ko rashin adalci ba.”

Abubkr Abdul Gama ya ce:

Kara karanta wannan

Trump ya kara nuna yatsa ga Najeriya, ya ce ba za a ji da dadi ba

“Idan dai har yayi wa Fulani laifi to su kai shi gaban kotu amma ba za ku ce a sauke shi daga mukaminsa ba. Ku yi korafi kuma a yanke hukunci yadda ya kamata.”

ADC ta aika sako ga Amupitan

A baya, mun wallafa cewa Jam’iyyar ADC ta yi kira ga Joash Ojo Amupitan, sabon shugaban INEC, da ya tabbatar da cewa nadin da shugaba Tinubu ya yi masa ya zama abin alheri.

Jam'iyyar ta bayyana cewa yayin da babban zaben 2027 ke karato wa, ya kamata Shugaban INEC ya ajiye dukkanin wani abin da ba dace ba domin tabbatar da sahihin zabe.

Jam’iyyar ta jaddada cewa har yanzu ba a san Amupitan sosai ba, don haka za ta sa ido sosai wajen ganin yadda zai jagoranci hukumar gabanin babban zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng