Wuta Ta Tashi a Kasuwar Singa da ke Kano da Sassafe, Shaguna Sun Kone
- Rahotanni sun tabbatar da cewa gobara ta tashi da sanyin safiyar Litinin a kasuwar Singa ta Kano, inda ta kona shaguna da dama
- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce kuskuren lantarki ne ya haddasa gobarar kuma an yi nasarar shawo kan matsalar
- Jami'an kashe gobara na jihar sun bayyana cewa ba a samu rahoton asarar rai ko daya ba, sai dai dukiya mai tarin yawa ta salwanta
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta kona shaguna 25 a kasuwar Singa da ke cikin birnin Kano.
Jami'an hukumar kashe gobara sun ce wutar ta haifar da babbar asara ta dukiya kafin a shawo kanta.

Source: Facebook
Leadership ta ce hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Talata.
Bayanin hukumar kashe gobara ta Kano
Saminu Yusif Abdullahi ya ce sun samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe daga wani mai suna Mubarak Muhammad wanda ya sanar da tashin wutar a cikin kasuwar.
A cewar Abdullahi:
“Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dr Alhaji Sani Anas, ta samu kiran gaggawa daga Mubarak Muhammad da misalin ƙarfe 5:00 na safe.
"Ya ce wuta ta tashi a kasuwar Singa. Nan take jami’anmu daga sassa daban-daban na Kano suka garzaya wurin.”
Ya ce da suka isa wurin, sun tarar da wani bene mai hawa ɗaya, wanda ake kira Alhaji Abdulmunafi Yunusa House, yana ci da wuta gaba ɗaya.
Ginin, wanda ke da fadin kafa 150 da 150, na dauke da shaguna da dama da ke gaban ginin da kuma a saman bene.
Shaguna sun kone a kasuwar Singa
Yayin da ya ke bayani game da shagunan da suka kone gobarar, Yusif Abdullahi ya bayyana wa jama'a cewa:

Kara karanta wannan
Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya
“Wutar ta kona shaguna 25 da ke gaban ginin da kuma dakuna 19 da ke saman bene.
"Sai dai jami’anmu sun yi nasarar kashe wutar kafin ta ƙone sauran shaguna 24 da ke sama, kuma duk shagunan da ke kasa sun tsira ba tare da lalacewa ba.”

Source: Twitter
Ya kara da cewa ma’aikatan sun fuskanci kalubale wajen shiga wurin gobarar saboda manyan motoci da tireloli da aka ajiye a kusa da kasuwar, wanda hakan ya kawo tsaiko a aikin ceto.
Dalilin tashin wuta a kasuwar Singa
Binciken farko da hukumar kashe gobara ta gudanar ya gano cewa matsalar lantarki ce ta jawo gobarar.
“Mun gana da shugaban gidan, Ambasada Garba Ibrahim Mai Maggie, da kuma wani mai tsaron gidan, Malam Ibrahim, wadanda suka tabbatar mana cewa akwai maɓallin wuta guda ɗaya da ke sarrafa dukkan gidan,”
Inji Abdullahi
Ya cigaba da cewa:
“Bayan bincike mai zurfi, mun gano cewa an yi amfani da maɓallin lantarki ba daidai ba, wanda hakan ya janyo matsalar da ta haddasa gobarar.”
ACFO Abdullahi ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a wannan gobara, sai dai shaguna da kaya masu daraja sun kone.
'Yan bindiga sun kai hari Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zargi 'yan bindiga masu garkuwa da mutane ne sun kai hari jihar Kano.
Yayin da suka farmaki wasu yankuna da ke kusa da iyakar jihar da Katsina, maharan sun yi nasarar sace mutane biyar.
An bayyana cewa dukkan wadanda suka dauka mata ne amma wasu daga cikinsu sun yi nasarar kubuta daga hannun 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng

