‘Kun Fi Tsoron Trump Sama da Allah’: Malamin Musulunci ga Manyan Arewa
- Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan azzaluman shugabannin Najeriya bayan Shugaba Donald Trump ya yi barazana ga kasar
- Malamin ya nuna takaici yadda wasu shugabanni suke tsoron Trump fiye da Allah, yana cewa hakan alamar azzalumai ne masu son duniya
- Ya roki Allah ya rikita azzalumai da ke goyon bayan masu ta’addanci kamar Bello Turji, yana addu’a Amurka ta samu nasara kansu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Murtala Bello Asada ya yi magana kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Malamin ya tabo maganar barazanar Donald Trump inda ya ce azzaluman shugabanni a Najeriya sun ji kunya.

Source: Facebook
Sheikh Asada ya dura kan azzaluman Najeriya
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya Litinin 10 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Sheikh Asada ya ce azzalumai a Najeriya suna tsoron shugaban Amurka, Donald Trump fiye da Allah mahalicci.
Ya ce:
"Kun ga miyagu azzalumai, makiya Allah hankalinsu ya tashi sun rikice, idan ba ku manta ba, shekaran jiya na fada muku azzaluman Najeriya sun fi jin tsoron Trump sama da Allah.
"Ku duba shugaban kasar Amurka ya yi magana sun rude, hankalinsu a tashi, wannan yana nuna Allah yana da abubuwan da yake rikita azzalumai.
"Allah ka kara riktia su, ka rikita azzalumai, muna rokon ka ka kawo mana zaman lafiya a kasarmu, wannan wa'azi ne sai mai hankali zai gane gaskiya."

Source: Facebook
Murtala Asada ya daura laifi kan manyan Arewa
Sheikh Murtala Bello ya ce manyan Arewa sun ji kunya saboda ba su da kishin yankinsu kamar yadda yan Kudu suka nuna suna da manya.
Ya ce ko mutum bai san me yake yi ba, ya san babu wadanda suka zalunci Musulunci da yankin Arewa face manyan yankin.
Ya kara da cewa:
"Ana nuna mana cewa manyan Arewa ko suna so ba su so sun ji kunya, mutanen Kudu sun nuna suna da manya.
"Sai gashi manyan Arewa sun zo suna kame-kame, wai an taso wa Musulunci, an taso muku din, yanzu hankalinku ya tashi saboda dukiyoyinku da ke kasashen waje.
"Tallafi da ake samowa daga kasashen waje shi ne tashin hankalin Najeriya, wallahi ko ka ki ko kaso mutanen Arewa su suka zalunci al'ummar Musulmin Arewacin Najeriya."
Malamin ya koka kan yadda azzalumai suka tayar da hankulansu game da barazanar Trump inda ya yi addu'ar Allah ya ba Amurka sa'a kan masu daurewa Bello Turji gindi.
Murtala Bello ya soki sulhu da Turji
A baya, an ji cewa malamin addinin musulunci, Sheikh Murtala Bello Asada, ya yi fatali da batun yin sulhu da jagoran 'yan bindiga, Bello Turji.
Sheikh Asada ya bayyana cewa ya kamata mutane su tashi su kare kansu maimakon tattauna da 'yan ta'adda marasa amana.
Hakazalika ya kuma karyata wani faifan murya da ake yadawa yana tattaunawa da Turji, inda ya ce tsoho ne ba na yanzu ba ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

