Ko Me Ya Yi Zafi: Sojoji Sun Budewa 'Yan Sandan da Ke Dawowa daga Zaben Anambra Wuta
- An samu rashin fahimtar juna tsakanin dakarun sojojin Najeriya da wasu jami'an 'yan sanda a jihar Anambra
- Sabanin da aka samu tsakanin jami'an tsaron guda biyu, ya jawo sojoji sun yi harbi kan 'yan sanda wadanda ke dawowa daga wajen zaben Anambra
- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Anambra, ya yi karin haske kan yadda lamarin ya auku da matakan da aka dauka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Sojoji a wani shingen bincike da ke kan titin Onitsha sun bude wuta kan wasu ’yan sanda a jihar Anambra.
Jami'an 'yan sandan dai suna dawowa ne daga aikin zaben gwamnan jihar Anambra da aka kammala a karshen mako.

Source: Twitter
A cewar rahoton Sahara Reporters, rikici ya barke tsakanin jami’an tsaron biyu ne lokacin da ’yan sanda suka isa shingen binciken sojojin a ranar Lahadi, yayin da suke dawowa daga aikin zabe.
Sojoji sun harbi 'yan sanda
Wani dan sanda ya samu harbin bindiga a kirji, yayin da wasu da dama suka ji rauni.
A cikin wani bidiyon da aka gani, an ga wasu ‘yan sanda suna kokarin ceto wani jami’i da ke zubar da jini, inda suke amfani da tufafi wajen toshe jinin da ke fita daga kirjinsa.
Wani dan sanda a cikin bidiyon ya ce:
“Yanzu haka abin da ke faruwa kenan yayin da muke dawowa daga aikin zaben jihar Anambra. Mun samu rashin jituwa da sojoji a shingen bincike, kafin mu ankara, sai suka bude mana wuta."
"An harbi daya daga cikinmu kai tsaye a kirji, wasu kuma sun ji rauni da dama.”
An tabbatar da aukuwar lamarin
Mai magana da yawun ‘yan sanda a Anambra, Ikenga Tochukwu Anthony, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Premium Times.
Ya bayyana cewa tuni aka warware rashin jituwar da aka samu a tsakanin bangarorin biyu.

Kara karanta wannan
Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji
Ya kara da cewa jami’in da aka harba ya farfado, kuma an sasanta lamarin tsakanin rundunonin biyu.
Sai dai kakakin rundunar sojin Najeriya, Kanal Appolonia Anele, ba ta amsa kiran waya ko sakon da aka aike mata ba a lokacin rahoton.
An tura 'yan sanda zuwa Anambra
Tun kafin zaben, Sufeto Janar na ‘han sanda, Kayode Egbetokun, ya sanar da cewa jami’an ‘yan sanda 45,000 za a tura su don samar da tsaro a zaben gwamnan Anambra.

Source: Facebook
Gwamna Charles Soludo na jam’iyyar APGA ya lashe zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.
A sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar, Soludo ya samu kuri’u 422,664, inda ya doke dan takarar jam’iyyar APC, Nicholas Ukachukwu, wanda ya samu kuri’u 99,445, tare da lashe dukkan kananan hukumomi 21 a jihar.
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan 'yan ta'addan a jihohin Borno, Kwara da Katsina.

Kara karanta wannan
Bidiyo: Rigima ta barke tsakanin mataimakin gwamna da sojan Najeriya a wajen zabe
Sojojin saman wadanda suka yi amfani da jiragen yaki wajen kai hare-haren sun hallaka 'yan ta'addan ISWAP da dama a jihar Borno.
Hakazalika sun ragargaji 'yan ta'adda da ke addabar mutane da hare-hare a jihohin Kwara da Katsina.
Asali: Legit.ng
