Uwargidan Tinubu da Matasan Kiristoci Sun Cimma Matsaya kan Ikirarin Shugaban Amurka

Uwargidan Tinubu da Matasan Kiristoci Sun Cimma Matsaya kan Ikirarin Shugaban Amurka

  • Zargin kisan kiristoci na ci gaba da daukar hankulan mutane musamman bayan barazanar Amurka na kawo farmaki Najeriya
  • Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta musanta zargin, tana mai cewa babu kanshin gaskiya a ciki
  • Kungiyar matasan kiristoci ta Najeriya ta bayyana cewa ana kashe musulmi ana kashe kiristoci, don haka zargin ba gaskiya ba ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu da kungiyar matasan kiristocin Najeriya sun cimma matsaya kan zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Hakan dai ya biyo bayan matakin da shugaban Amurka, Donald Trump ya dauka na sanya Najeriya a jeirn kasashen da ake tauye wa mutane 'yancin addini.

Matar shugaban kasa.
Hoton uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu Hoto: @OluremiTinubu
Source: Facebook

Matar Tinubu ta karyata kisan kiristoci

Jaridar Vanguard ta tattaro cewar uwargidan shugaban kasa ta yi fatali da hakan, tana mai cewa zargin da ake yi na kisan kiristoci a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Babachir ya fasa kwai kan rawar da Buhari da Tinubu suka taka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oluremi Tinubu ta bayyana hakan ne a taron shugabannin kungiyar Youth Wing of CAN na ƙasa da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin.

Matar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Misis Salamatu Gbajabiamila ce ta walilci uwargidan shugaban kasa a wurin taron.

“Gaskiya ita ke ‘yantarwa, tana warkar da raunuka, tana kuma haɗa zukata cikin zumunci. Mu zaɓi haɗin kai maimakon rabuwar kawuna, mu kuma tashi tsaye wajen yakar wariyar addini da kabilanci,” in ji uwargidan Tinubu.

Ta kara da cewa ƙarƙashin manufar “Renewed Hope Agenda” ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa matakan kare rayuka da dukiyoyi.

“Ina kira ga matasan Kirista da su riƙe gaskiya a matsayin jagora, duk gidan da ya kasu biyu ba zai iya tsayuwa ba.
"Ku nemi ilimi domin shi ne fitilar da ke jagorantar kowa zuwa ga gaskiya," in ji ta.

Matasan CAN sun yi fatali da ikirarin Trump

Kara karanta wannan

"Ina matashi dan Shekara 40," Obasanjo ya tuna zaman da ya yi da Amurka a mulkin soja

A nasa jawabin, Belusochukwu Enwere, shugaban kungiyar matasan Kirista (YOWICAN), ya ce matakin Amurka bai yi daidai da abubuwan da ke faruwa a Najeriya ba.

“Wannan lokaci ne da ba ya buƙatar jayayya ko tsaurin ra’ayi, face tattaunawa da fahimta.
"Gaskiya ce kadai za ta fitar da mu daga labaran da ke nuna mu a matsayin masu aikata laifi maimakon masu kare jama’a,” in ji shi.
Trump da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban Amurka, Donald Trump da na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Getty Images

Ya nuna alhini kan kisan jama’a a Filato, Benue, Kaduna, da wasu jihohi, yana mai cewa “ciwon ɗaya ne ga dukkan al’ummar Najeriya, ba laifin addini ko kabila ba.”

“A daina kashe Kiristoci. A daina kashe Musulmai. A daina kashe ‘yan Najeriya gaba ɗaya. Kowace rai tana da daraja, kuma kowanne ɗan ƙasa ya cancanci kariya,” In ji Enwere.

Babachir ya goyi bayan Trump

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya goyi bayan shugaban Amurka, Donald Trump kan kisan kiristoci a Najeriya.

Babachir Lawal ya ce kiristocin da suka kai korafi Amurka domin ta kawo masu dauki ba su yi laifi ba saboda gwamnati ta gaza kare su.

Kara karanta wannan

Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Ya kuma koka cewa sojojin Najeriya na ci gaba da rasa rayukansu saboda rashin kayan yaƙi na zamani, yayin da ‘yan ta’adda ke amfani da manyan makamai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262