Kisan Kiristoci: Tsohon Sakataren Gwamnatin Najeriya Ya Goyi Bayan Shugaban Amurka
- Babachir Lawal ya ce kiristocin da suka kai korafi Amurka domin ta kawo masu dauki ba su yi laifi ba saboda gwamnati ta gaza kare su
- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce duk da ana kashe musulmai a Najeriya, amma shi yan uwansa kiristoci kadai ya damu da su
- Ya ce babu dalilin da gwamnatin Najeriya za ta ga laifin wadanda suka fita kasashen waje domin neman dauki tun da ta gaza samar da tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, ya goyi bayan shugaban Amurka, Donald Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya.
Babachir ya ce korafin da wasu 'yan Najeriya suka kai Amurka domin a kawo masu dauki ba laifi ba ne domin gwamnatin Najeriya ta gaza kare su.

Kara karanta wannan
"Ina matashi dan Shekara 40," Obasanjo ya tuna zaman da ya yi da Amurka a mulkin soja

Source: Facebook
Babachir Lawal ya faɗi haka ne a lokacin da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Television a daren Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babachir ya soki gwamnatin Najeriya
Ya ce gwamnatin Najeriya ba ta da hurumin zargin ‘yan ƙasa da neman taimako daga waje idan ta kasa samar da tsaro a cikin ƙasa.
Ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar ta kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa idan tana son su daina kiran taimako daga ƙasashen waje.
“Gwamnati ta tabbatar mana cewa tana iya ba mu kariya, tsaro, da cigaban da muke fata. Idan ba za su iya ba, to ba su da hujjar zargin kowane ɓangare na al’umma da neman taimako daga ko’ina,” in ji shi.
Dalilan Babachir na goyon bayan Trump
Tsohon sakataren ya kuma goyi bayan matsayar Shugaba Trump, wanda ya bayyana cewa kisan Kiristoci a Najeriya ya kai matsayin “kisan kare dangi."
“Wannan kisan kare dangi ne. Idan ba haka ba, to kisan gilla ne,” in ji Babachir.

Kara karanta wannan
Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Ya ce hujjar da wasu ke bayarwa cewa “an fi kashe Musulmai fiye da Kiristoci” ba ta kawar da gaskiyar abin da ke faruwa ba, cewar Vanguard.
“Wannan hujja ce marar ma’ana. Wadanda suka fi ƙarfi wajen musanta batun su ne Musulmai, saboda ‘yan’uwansu ne ke aikata wannan kisa.
"Idan yara dubu ɗaya aka kashe, ɗaya daga cikinsu ɗanka ne, hankalinka zai tashi ne kawai kan ɗanka, ba sauran ba,” in ji shi.
Tsohon SGF ɗin ya kuma koka cewa sojojin Najeriya na ci gaba da rasa rayukansu saboda rashin kayan yaƙi na zamani, yayin da ‘yan ta’adda ke amfani da makamai masu ƙarfi.

Source: Twitter
Babachir ya sake taso Shugaba Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ya sake taso shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a gaba kan matsalar rashin tsaro.
Babachir Lawal wanda ya yi aiki a gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta da niyyar magance matsalar tsaro.
Ya ce kafin Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, jihar da ya fito watau Adamawa ta kasance cikin kwanciyar hankali, amma yanzu tsaro ya tabarbare fiye da baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng