Malamai Sun Fadawa Tinubu Hanyar Magance Rashin Tsaro da Zafafan Addu'o'i
- Malaman addinai sun bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana ranar addu’a da azumi ta kasa domin neman taimakon Allah kan ta’addanci
- An gudanar da zaman addu’ar hadin kai a Birnin Kebbi, karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris tare da malaman Musulmi da Kiristoci
- Masu addu’ar sun yaba da kokarin gwamnan wajen yaki da rashin tsaro tare da kira ga shugaba Tinubu da sauran ‘yan kasa su hada kai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kebbi – Jagororin addinai daga bangarorin Musulunci da Kiristanci sun bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana rana ta kasa don addu’a da azumi.
Sun bukaci a yi haka ne domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar Arewa.

Kara karanta wannan
Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu suka bullo wa barazanar harin Amurka sun fara jan hankali

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa bukatarsu ta fito ne yayin taron addu’a ta hadin kai da gwamnatin Jihar Kebbi ta shirya a ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron addu'ar wani bangare ne na shirin gwamna Nasir Idris na kawo karshen matsalar tsaro a Kebbi da kasa baki daya.
An yi taron addu’a a Birnin Kebbi
Taron ya samu halartar fitattun malamai da shugabannin addinai, ciki har da malamai daga dukkan bangarori na addinin Musulunci da kuma limaman coci daga mazhabobi daban-daban.
Gwamna Nasir Idris ya jaddada kudirin gwamnatinsa na tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro, yana mai cewa haduwar Musulmi da Kiristoci a wannan lokaci alama ce ta hadin kai.
“Ina kira gare mu da mu ci gaba da zama daya, mu yi addu’a tare don samun zaman lafiya da adalci a kasar mu,”
Inji gwamna Nasir Idris
Malaman da suka halarci taron addu'ar
Daga bangaren Musulmi, malamai da suka jagoranci addu’a sun hada da Sheikh Abdulrahaman Isah Jega, Sheikh Abbas Muhammadu Jega, Sheikh Umar Malisa, da Sheikh Abubakar Ribah.

Kara karanta wannan
Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya
Daga bangaren Kiristoci kuwa, mataimakin shugaban kungiyar CAN a Kebbi, Fasto Femi Oropin, ya jagoranci addu’a tare da Fasto Nuhu Mamman Gudul, Fasto Joshua Ochimana.
Dukkan su sun jaddada bukatar hadin kai a tsakanin al’umma don tabbatar da tsaro da kuma magance rikice-rikice.
Yabon gwamnan Kebbi da kira ga Tinubu
Rahoton New Telegraph ya nuna cewa limaman addinai sun yaba wa Gwamna Idris bisa “kudirin sa mai karfi na yaki da ta’addanci” a Kebbi da jihohin makwabta.

Source: Facebook
Sun tuna yadda gwamnan ya karbi bakuncin manyan tarukan tsaro kamar na majalisar sarakunan gargajiya ta Arewa, gwamnonin APC da saurasu domin inganta matakan tsaro.
Gwamnatin jihar ta kara wa jami’an tsaro karfi ta hanyar samar da motoci 100 na sintiri da babura 5,000 don kula da yankunan da ke cikin hadari.
A cikin kudirinsu na karshe, limaman addinai sun roki Shugaba Bola Tinubu da ya shirya addu’a ta kasa ta hadin kai game da matsalar tsaro.
'Yan bindiga sun kai hari Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari jihar Kano dauke da makamai.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace muta 5 yayin harin, amma wasu sun kubuta a hannunsu.
Mutanen karamar hukumar Shanono da ke fuskantar matsalar sun yi kira ga gwamnati ta kawo musu dauki kan lamarin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
