Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu Suka Bullo Wa Barazanar Harin Amurka Sun Fara Jan Hankali

Hanyoyin da Tinubu da Nuhu Ribadu Suka Bullo Wa Barazanar Harin Amurka Sun Fara Jan Hankali

  • Gwamnatin Tarayya na ci gaba da daukar matakan kauce wa barazanar shugaban Amurka, Donald Trump ta kai hari Najeriya
  • Wata kungiya ta yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Malam Nuhu Ribadu bisa yadda suka bullo wa lamarin cikin hikima
  • Kungiyar ta jaddda manufarta na hada kan yan kasa domin bunkasa zaman lafiya da kare martabar Najeriya a idon duniya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar The Citizens Project ta yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Mai Ba da Shawara kan Tsaro na Ƙasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu.

Kungiyar ta yabi jagororin biyu ne bisa yadda suka kwantar da hankali da hikimar da suka nuna wajen martani ga maganganun Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump.

Malam Nuhu Ribadu da Bola Tinubu.
Hoton mai va da shawara kan tsaron kasa, Malam Nuhu Ribadu da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Nuhu Ribadu, @OfficialABAT
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da aka tura wa Leadership, shugaban ƙungiyar, A’dab Ukor, ya bayyana cewa Najeriya da Amurka suna da doguwar alaƙa mai kyau.

Kara karanta wannan

Minista ya fadawa 'yan Najeriya abin da za su yi bayan barazanar Donald Trump

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiya ta yaba wa Gwamnatin Tinubu

A cewarssa, Najeriya da Amurka kawayen juna ne da suka dade suna girmama juna,, ra’ayoyin dimokuraɗiyya da burin samar da zaman lafiya da ci gaba.

Sanarwar ta ce:

“Duba da haka muke ganin cewa tattaunawa da haɗin kai mai ma’ana su ne hanyoyin da suka fi dacewa wajen fuskantar barazanar tsaro a gida da na ƙasa da ƙasa.”
“Ayyukan ta’addanci da suka addabi wasu yankuna na Najeriya fiye da shekaru 15 ya shafi al’ummomi masu addinai da kabilu daban-daban.
"Amma tun bayan hawan gwamnatin Tinubu a 2023, an samu ci gaba mai kyau sakamakon ingantaccen tsari, dabarun leken asiri, da ƙarfafa ayyukan tabbatar da zaman lafiya a al’umma.”

An bukaci hadin kan Najeriya da Amurka

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta haɗa kai da Najeriya ta hanyar ƙarfafa hanyoyin haɗin gwiwa maimakon yin amfani da kalmomi da za a iya fassara su da kuskure.

Kara karanta wannan

Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya

A rahoton Daily Post, kungiyar ta kara da cewa:

“Hanya mafi inganci ta cimma burin kawar da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa ita ce ta hanyar haɗin kai a fannonin musayar bayanan leken asiri, horo da tallafin fasaha.
"Muna sake tabbatar da cikakken goyon bayanmu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, mai ba da shawara kan tsaro na Ƙasa, da hukumomin tsaro bisa jajircewarsu wajen kare rayukan ‘yan ƙasa, tabbatar da zaman lafiya, da kare ƙasarmu.”
Shugaban Amurka, Donald Trump.
Hoton shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: @realDonaldTrump
Source: Twitter

A ƙarshe, kungiyar ta bayyana cewa The Citizens Project a shirye take wajen “ƙarfafa zaman lafiya, gaskiya, da ci gaba."

A cewarta, za kuma ta ci gaba da neman haɗin kai tsakanin gwamnati, ‘yan ƙasa, da ƙasashen duniya domin bunƙasa zaman lafiya, cigaba, da kare martabar Najeriya a idon duniya.”

Obasanjo ya tuna alakarsa da Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce lokacin mulkinsa, Amurka ba ta yin gaba kanta ta yi wani abu a nahiyar Afirka sai ta fada masa.

Kara karanta wannan

'Ku dawo gida,' Shehu Sani ya aika sako ga wasu ƴan Najeriya da ke zaune a Amurka

Obasanjo ya bayyana cewa a wancan lokacin, Amurka ta dauki Najeriya a matsayin kasa mai tasowa kuma wacce za ta jagoranci nahiyar Afirka.

Duk bai ambaci Trump kai tsaye ba amma ana ganin kalaman Obasanjo na da alaka da barazanar da ya yi ta kawo daukin soji Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262