'Yan Gida 1 Sun Arce daga Hannun 'Yan Bindiga yayin da Bacci Ya Sace Miyagun

'Yan Gida 1 Sun Arce daga Hannun 'Yan Bindiga yayin da Bacci Ya Sace Miyagun

  • ‘Yan uwa biyu, Isaac da Victor Olayere, da aka sace a kan titin Adughe–Imoga, sun kuɓuta bayan 'yan bindiga sun yi barci
  • An ce 'yan uwan sun kubuto ne bayan masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 22 matsayin kudin fansa daga iyalansu
  • Wani basarake a Edo ya bukaci gwamnati da ta kafa ofishin ‘yan sanda a yankin don magance matsalar sace sacen mutane

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Edo - Wasu 'yan gida daya su biyu da aka sace a yankin Adughe–Imoga na jihar Edo sun samu nasarar tserowa daga hannun masu garkuwa da mutane.

An rahoto cewa, 'yan gida dayan sun arce daga hannun 'yan bindigar ne bayan bacci ya yi awon gaba da miyagun a sansanin da aka daure su.

'Yan gida 1 sun kubuto daga hannun 'yan bindiga suna cikin yin bacci
Taswirar jihar Edo da ke Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan gida 1 sun tsere daga hannun 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Abuja: Wike ya taso masu kadarori a gaba, ya ba su kwanakin biyan tarar N5m

Jaridar Punch ta rahoto cewa masu garkuwar sun sace Isaac da Victor Olayere ne a ranar 8 ga Nuwamba, a yankin Uma/Imoga da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sace 'yan gida dayan, masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa har Naira miliyan 22, lamarin da ya jefa al'ummar yankin a cikin firgici.

A yayin da iyalansu ke ƙoƙarin tara kuɗin, yaran biyu sun kira mahaifinsu da wata lambar waya da ba a sani ba, inda suka sanar masa cewa sun tsere daga hannun 'yan bindigar.

Sarkin Imoga ya tabbatar da kuɓutarsu

Okpahi na masarautar Imoga, Oba Patrick Obajoye, ya tabbatar da faruwar lamarin a hirarsa da jaridar The Punch ta wayar tarho ranar Litinin.

Oba Patrick Obajoye ya ce an sanar da ‘yan sanda da ke ofishin 'yan sanda na Ibillo, inda ake sa ran za a hada kai wajen kubutar da wadanda aka sace.

“An sace ‘yan gida dayan a ranar 8 ga Nuwamba a kan titin Adughe–Imoga, aka kai su cikin daji. Masu garkuwar sun kira iyalansu suka nemi N22m na kudin fansa.

Kara karanta wannan

Kogi: Jama'a sun barke da zanga zanga bayan 'yan bindiga sun jefa gawar tsohuwa a daji

"Amma daga baya aka ce masu garkuwar sun yi bacci mai nauyi a cikin dajin, wanda ya bai wa wadanda aka sace damar tserewa."

- Oba Patrick Obajoye.

Ya ce daga baya ‘yan sa-kai daga Adughe, wani gari a jihar Kogi suka tsinci yaran a cikin daji, inda a garin Imoga, matasa suka shiga don yin arangama da 'yan bindigar, amma aka tarar ba sa nan.

An roki gwamnati ta kafa ofishin 'yan sanda a garin Imoga da ke jihar Edo saboda matsalar tsaro.
Sababbin motocin sulke da gwamnati ta ba rundunar 'yan sanda. Hoto: @ubasanius
Source: Twitter

Sarki ya bukaci gwamnati ta kafa ofishin ‘yan sanda

Oba Obajoye ya koka da yadda matsalar sace mutane da hare-haren makiyaya masu dauke da makamai ke yawaita a yankin.

Basaraken ya bayyana cewa:

“Muna bukatar a kafa ofishin ‘yan sanda a nan Imoga. Idan hakan ta faru, jami’ai za su rika sintiri a kai a kai don tabbatar da tsaron jama’a.”

Ya kara da cewa Imoga ita ce mafi girman ƙauye a Akoko Edo, kuma tana da muhimmanci wajen haɗa jihar Edo da yankin Arewacin ƙasar.

Masana sun ce duk da kokarin Gwamna Monday Okpebholo wajen inganta tsaro, garkuwa da mutane na ci gaba da zama kalubale mai tsanani a jihar.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi arangama da 'yan ta'adda a Borno, an kubutar da mutane 86

Mutane 3 sun tsere daga hannun 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, yayin da mahara su ka yi tatil da giya su na bacci, wasu daga cikin wadanda suka kama sun tsere da tsakar dare.

Mutanen uku daga cikin 11 da aka yi garkuwa da su sun tsere ne a daren ranar Juma’a a kauyen Azzara da ke jihar Kaduna.

Maharan sun farmaki Unguwar Tudu a kauyen inda suka hallaka soja da kuma garkuwa da mutanen guda 11 tare da mai gida da iyalinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com