Lokaci Ya Yi: Matar Marigayi Shehu Shagari da Ta Rage a Duniya Ta Rasu
- Allah ya yi wa matar tsohon shugaban kasan Najeriya, marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, rasuwa a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025
- Hajiya Sutura Shehu Shagari ta kasance matar tsohon shugaban kasan ta karshe da ta rage a duniya kafin rasuwarta
- A cikin sanarwar da iyalan tsohin shugaban kasan suka fitar, sun bayyana cewa raauwar marigayiyar ta girgiza su matuka
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Sokoto - Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar marigayi tsohon shugaban kasa,Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, ta rasu.
Hajiya Sutura Shehu Shagari ta yi bankwana da duniya ne tana da shekaru 89.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban iyalan Shagari, Kyaftin Muhammad Bala Shagari (mai ritaya), ya fitar a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar Shehu Shagari ta rasu

Kara karanta wannan
Lokaci ya yi: Matar tsohon shugaban Najeriya, Shehu Shagari ta riga mu gidan gaskiya
Sanarwar ta tabbatar da cewa Hajiya Sutura ta rasu ne da misalin karfe 3:00 na rana bayan doguwar jinya, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.
"Cikin alhini muke sanar da rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar marigayi tsohon shugaban kasar tarayyar Najeriya, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari GCFR, Turakin Sokoto."
“Hajiya Sutura ta rasu yau da misalin karfe 3:00 na rana tana da shekaru 89 bayan doguwar jinya.”
- Muhammad Bala Shagari
Sanarwar ta bayyana Hajiya Sutura a matsayin uwa mai cike da mutunci, mai tawali’u wadda ta rayu cikin nutsuwa da tausayi ga jama’a.
A cewar sanarwar rasuwarta ta girgiza iyalan Shagari da abokan arziki da dama.
"Shirye-shirye kan jana'iza da cikakkun bayanai za su biyo baya. Allah Ya jikanta da rahama."
- Muhammad Bala Shagari
Waye marigayi Shehu Shagari?
Hajiya Sutura ita kadai ce ta rage a duniya daga cikin matan Shehu Shagari, wanda shi ne shugaban kasa na farko da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya a Najeriya daga 1979 zuwa 1983 karkashin jam’iyyar NPN.
An haifi marigayi Shehu Shagari a ƙauyen Shagari, jihar Sakkwato, a ranar 25 ga Fabrairu, 1925.

Source: Facebook
Ya kasance malami, jami’in gwamnati, ɗan siyasa wanda ya rike mukamai da dama kafin ya zama shugaban kasa.
Gwamnatinsa ta mai da hankali kan gidaje, ilimi, noma, da masana’antu karkashin shirin “Green Revolution.”
Sai dai mulkinsa ya kare a ranar 31 ga watan Disamba, 1983, bayan juyin mulki da Manjo-Janar Muhammadu Buhari ya jagoranta a wancan lokacin.
Marigayi Shehu Shagari ya rasu a ranar, 28 ga watan Disamba, 2018, yana da shekaru 93 a duniya.
Babban malamin addinin Musulunci ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Allah ya yi wa babban malamin addinin Musulunci a garin Funtua na jihar Katsina, Sheikh Goni Imam Sa'id Musa, rasuwa.
Marigayi malamin, wanda shi ne babban limamin masallacin 'yan izala da ke garin Funtua (JIBWIS) ya rasu ne ranar Lahadi da daddare bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya.
Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu a majalisar dattawa, Mukhtar Dandutse, ya ce rasuwar malamin babban rashi ne ga mutanen Funtua, jihar Katsina, da kuma al'ummar musulmi baki daya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
