Tinubu Ya Aika Sakon Taya Murna ga Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau
- Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya cika shekara 70 da haihuwa a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2025
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya Malam Shekarau murna tare da fatan zai ci gaba da ba da gudummuwa wajen gina kasa
- Tinubu ya yi waiwaye kan rayuwar Malam Ibrahim Shekarau, wanda ya taso tun daga malamin makaranta har zuwa kujerar gwamnan Kano
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, murnar cika shekaru 70 da haihuwa a duniya.
Bola Tinubu ya bayyana Malam Shekarau a matsayin jigo kuma jagoran da ya zama abin koyi, wanda ya gudanar da mulki cikin gaskiya da rikon amana.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya fitar yau Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya
Shugaba Tinubu ya tuna mulkin Shekarau
Shugaba Tinubu ya yi waiwaye kan gudummuwar da Shekarau ya ba da wajen kawo ci gaba ga kasa tun daga lokacin da yake malamin makaranta har zuwa lokacin da ya zama babban sakatare a ma'aikatar gwamnati a Kano.
Shugaban ƙasar bai tsaya iya nan ba, ya kuma tuna da nasarar Shekarau a zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2003, wacce ta kafa tarihi a siyasar jihar.
Tinubu ya ce gwamnatin Shekaru ta yi fice saboda yadda ya gudanar da mulkin jin ƙai da mai da hankali ga bukatun jama’a, wanda ya sa mutane da dama a jihar da ma sauran sassan ƙasa suka yaba masa.
Ya kara da cewa Shekarau ya ci gaba da yi wa kasa hidima ga bayan ya bar mulkin Kano a 2011, inda ya yi aiki a matsayin Ministan Ilimi daga 2014 zuwa 2015.
Sannan kuma Malam Ibrahim Shekaru ya rike kujerar Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya daga 2019–2023.

Kara karanta wannan
Sokoto: Gwamnati ta musanta sakaci kan harin 'yan bindiga, ta bayya yadda lamarin yake
Tinubu ya yi wa Shekarau fatan alheri
Bola Tinubu ya kara yabawa Shekarau, yana mai cewa, “ya nuna kwarewa da gaskiya a duk mukamin da ya rike a rayuwarsa."
Shugaban ƙasar ya gode wa Sanata Shekarau biaa gudunmawarsa a matsayin malami, ma’aikacin gwamnati, da ɗan siyasa, yana mai cewa nasarorinsa na ci gaba da zama abin koyi ga matasa a fadin ƙasa.
A ƙarshe, Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, natsuwa da jagoranci, tare da fatan zai ci gaba da kasancewa ginshiƙi a hidimar jama’a da ƙasa baki ɗaya.

Source: Facebook
Tinubu ya taya Gwamna Soludo murna
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon taya murna ga Gwamna Charles Chikwuma Soludo bisa nasarar da ya samu a zaben gwamnan Anambra.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa nasarar ta tabbatar da cewa tsare-tsaren gwamnatinsa suna haifar da sakamako mai kyau ga al’umma.
Tinubu ya kuma yaba wa mutanen Anambra, jami’an tsaro, da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) saboda yadda aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da gaskiya.
Asali: Legit.ng