Minista Ya Fadawa 'Yan Najeriya abin da Za Su Yi bayan Barazanar Donald Trump

Minista Ya Fadawa 'Yan Najeriya abin da Za Su Yi bayan Barazanar Donald Trump

  • Ministan labarai, Mohammed Idris ya roki ‘yan Najeriya su kwantar da hankali kan rikicin diflomasiyya da Amurka
  • Ya ce Shugaba Bola Tinubu na da ƙwarewar da ake bukata don kare martabar ƙasa da gyara dangantaka da ƙasashen waje
  • Wannan na zuwa ne bayan Amurka ta fara shirin kai hari Najeriya, abin da ya jawo martanin ƙasashe, ciki har da China

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jigawa -Ministan labarai, Mohammed Idris, ya bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu a yayin da ake fama da sabuwar takaddamar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka.

Mohammed Idris ya yi wannan kira ne lokacin da ya kai ziyara ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, a Dutse ranar Litinin.

Ministan labarai, Mohammed Idris ya bukaci 'yan Najeriya su kwantar da hankalinsu kan kalaman Trump.
Ministan labarai, Mohammed Idris ya na jawabi ga manema labarai a Abuja. Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Twitter

'Ku kwantar da hankalin ku' - Minista ga 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, mai magana da yawun ministan ya fitar, a ranar Litinin, in ji rahoton Punch.

Rabiu Ibrahim ya bayyana cewa ministan ya jaddada cikakken kwarin gwiwa ga shugabancin Bola Tinubu wajen kare ƙasar da kuma inganta dangantaka da ƙasashen duniya.

“Shugaba Bola Tinubu na da duk abin da ake buƙata don kare Najeriya daga masu neman tayar da hankali, da kuma gyara kowace matsala da ke tsakanin mu da abokan sauran ƙasasbe.
"Don haka, ‘yan Najeriya su kwantar da hankalinsu."

- Mohammed Idris.

Yadda kalaman Trump suka tayar da kura

An samu rashin jituwar ne bayan wani sako da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce Kiristoci a Najeriya suna fuskantar kisan kare dangi daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi na Musulmi.

“Dubban Kiristoci ne ake kashe wa. Ƙungiyoyin ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi ne ke da alhakin wannan kisan kiyashin.
"Don haka, na sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake da damuwa da su musamman,” in ji Donald Trump.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Jigo a APC ya gargaɗi ƴan adawa su iya bakinsu

Ya kuma bayyana cewa Amurka “ba za ta yi shiru yayin da irin wannan ta’addanci ke faruwa ba,” yana mai cewa gwamnatinsa “za ta kasance a shirye, don kare Kiristoci a duniya baki ɗaya.”

Gwamnatin tarayya ta ce a shirye take ta kare Najeriya daga koce matsala kuma kalaman Trump ba abin damuwa ba ne.
Hoton shugaban kasar Amurka, Donald Trump da na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @realDonaldTrump, @officialABAT
Source: Getty Images

Barazanar soji daga Amurka ta jawo ce-ce-ku-ce

A ranar 1 ga Nuwamba, Trump ya sanar da cewa ya ba da umarni ga Ma’aikatar Tsaro ta Amurka (Pentagon) da ta tsara “matakan soja” a kan ƙungiyoyin ta’addanci a Najeriya, wai don kare al’ummomin Kirista.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani cikin ladabi, inda ta ƙaryata zargin, tana mai cewa ƙasar tana mutunta ‘yancin yin addini kuma tana kare ‘yancin dukkan al’ummomi ba tare da bambanci ba.

Shugaba Bola Tinubu ya nanata cewa Najeriya ƙasa ce mai ‘yanci, wadda ke mutunta doka da walwala ta addinai, yana mai cewa ba za ta yarda da kowace ƙasa ta tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida ba.

China da Rasha sun nuna goyon baya ga Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, barazanar da Amurka ta yi ta jawo hankalin ƙasashen duniya, musamman China da Rasha, waɗanda suka goyi bayan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

China, Rasha dai ta nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, tare da kira ga Amurka da ta mutunta ‘yancin mulkin Najeriya da zaman lafiyarta.

Masu nazari sun ce wannan takaddama ta kara jaddada bukatar Najeriya ta ci gaba da yin mu’amala da ƙasashen duniya bisa mutunta juna da kare martabar ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com