Abubuwa da Ya Kamata Ku Sani game da Gwamna Soludo da Ya Lashe Zaben Anambra

Abubuwa da Ya Kamata Ku Sani game da Gwamna Soludo da Ya Lashe Zaben Anambra

  • Gwamna Charles Chukwuma Soludo na Anambra na daga cikin yan takara a zaben gwamnan gwamnan jihar
  • Bayan fafatawa, hukumar zabe ta INEC ta sanar da cewa Gwamna Charles Soludo da ya yi takara karkashin jam'iyyar APGA ya yi nasara
  • Soludo ya yi nasara ne domin ci gaba da wa’adin mulki na biyu karkashin jam’iyyar bayan kammala wa'adin mulkinsa na farko da ya fara a 2022

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - An fafata a jihar Anambra kan neman kujerar gwamna a ranar Asabar 8 ga watan Nuwambar shekarar 2025 da muke ciki.

Gwamnan Jihar Anambra kuma dan takarar jam’iyyar APGA, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya nemi wa’adin mulki na biyu a zaben 2025.

Muhimman abubuwa game da Gwamna Soludo
Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Facebook

Abubuwan sani game da Gwamna Soludo

Rahoton Channels TV ya ce hukumar INEC mai zaman kanta ta ayyana Charles Soludo a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Dan takarar LP ya bayyana abin da ya hana shi lashe kujerar gwamna

Soludo, wanda ya taba zama gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya hau mulki a shekarar 2022 bayan lashe zaben gwamna na 2021.

Tunaninsa na sake tsayawa takara ya samo asali ne daga jajircewa da kishin jiharsa ta Anambra kamar yadda ya sha fada a baya.

Legit Hausa ta yi duba kan wasu muhimman abubuwa takwas game da rayuwarsa da tafiyarsa a siyasa:

1. Tarihin rayuwar Soludo

An haifi Charles Soludo a ranar 28 ga Yuli, 1960 a garin Isuofia, karamar hukumar Aguata a Jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Soludo ya rasa mahaifiyarsa tun yana karami, wanda hakan ya shafi yadda ya taso a rayuwarsa.

2. Rayuwar iyalin Soludo

Gwamna Charles Soludo yana da iyalai inda ya auri Mrs. Nonye Soludo, kuma suna da ’ya’ya shida tare.

Kafin ya shiga siyasa, yana sirranta rayuwarsa daga kafofin labarai wanda ya kara ba shi damar gudanar da rayuwarsa cikin sauki.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi magana kan zaben Anambra, ya aika sako ga Gwamna Soludo

Gwamna Soludo ya lashe zaben gwamnan jihar Anambra
Gwamna Charles Soludo na Anambra. Hoto: @ccSoludo.
Source: Twitter

3. Tafiyar siyasar Soludo

Gwamna Soludo ya fara neman kujerar gwamna a 2019 karkashin jam’iyyar PDP amma ya sha kaye.

Daga baya ya koma APGA a 2013, sai dai an hana shi tsayawa takara a wancan lokaci, kamar yadda Punch ta ruwaito.

A 2021, ya sake tsayawa, inda ya lashe zaben bayan kammala sauran zabubbuka a kananan hukumomi 19 daga cikin 21, da kuri’u 112,229.

4. Ilimi da nasarorin karatu

Farfesa Soludo ya kammala digirinsa na farko da sakamako mai kyau a 1984, ya samu digiri na biyu (MSc) a 1987 da PhD a 1989.

Ya yi karatu a tsanagayar tattalin arziki a Jami’ar Najeriya Nsukka a jihar Enugu, inda daga baya ya zama Farfesa.

5. Ayyukan koyarwa da kasashen duniya

Charles Soludo ya taba koyarwa a jami’o’i da cibiyoyi kamar IMF, Cambridge, Oxford, da kuma Brookings.

Ya yi aiki a matsayin farfesa da ya ke kai ziyara a Kwalejin Swarthmore , Amurka, a 1999, ya kuma ba da shawara ga cibiyoyi irin su Bankin Duniya da UNDP.

Kara karanta wannan

Gwamna Soludo ya aika sako ga Tinubu bayan lallasa dan takarar APC a zaben Anambra

6. Rawarsa a matsayin gwamnan CBN

Charles Chukwuma Soludo ya zama Babban Mashawarcin Tattalin Arziki ga Shugaba Olusegun Obasanjo a 2003, kafin ya zama gwamnan CBN a 2004.

Shi ne ya jagoranci gyaran tsarin bankuna da kafa Africa Finance Corporation (AFC) wanda hakan ya taimaka kwarai game da bunkasar tattalin arziki.

Kafin CBN, Soludo ya rike mukamin Babban Darakta a Hukumar Tsarin Kasa, a 2008, ya yi hasashen cewa za a rage yawan bankuna a Najeriya kafin karshen shekarar.

Yan Anambra sun sake zaben Charles Soludo
Gwamnan Anambra Charles Soludo na jihar Anambra. Hoto: @ccSoludo.
Source: Facebook

7. Mukamin da Buhari ya ba shi

A 2019, Marigayi Muhammadu Buhari ya nada shi cikin kwamitin masu ba da shawara kan tattalin arziki, wanda ke ba da rahoto kai tsaye ga fadar shugaban kasa.

Soludo ya rike mukamin ne shekaru uku kafin rantsar da shi a matsayin gwamnan Anambra wanda ya yi nasara, cewar TheCable.

8. Hari a lokacin kamfe

A watan Afrilu 2021, ’yan bindiga suka kai masa hari yayin taro a garinsu na Isuofia, inda ’yan sanda uku suka mutu.

Kara karanta wannan

Zaben Anambra: Abin da Soludo ya ce bayan samun wa'adi na 2

Ya ce lamarin “ba shi da ma’ana,” kuma ya sadaukar da nasarar zabensa ga jami’an da suka rasa rayukansu.

Soludo ya godewa Tinubu bayan lashe zabe

Mun ba ku labarin cewa mutanen jihar Anambra sun sake zaben Gwamna Charles Chukwuma Soludo a matsayin wanda zai ci gaba da mulkarsu har na tsawon shekara hudu.

Gwamna Soludo ya nuna matukar godiyarsa ga mutanen jihar kan amanar da suka sake damkawa a hannunsa.

Hakazalika, Gwamna Soludo ya aika da sako ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayn nasarar da ya samu a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.