Malaman Addinin Musulunci a Kano Sun ba da Mafita kan Shirin Amurka na Kawo Farmaki Najeriya

Malaman Addinin Musulunci a Kano Sun ba da Mafita kan Shirin Amurka na Kawo Farmaki Najeriya

  • Malamai na ci gaba da tsokaci kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na kawo farmaki Najeriya don kare kiristoci
  • Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta jihar Kano ta bukaci yan Najeriya su tashi tsaye, su dage da addu'a don samun kwanciyar hankali
  • Sheikh Ibrahim Khalil ya bukaci a bar shugabannin siyasa da na addinai su lalubo mafita kan wannan lamari da ya tada hankulan jama'a

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta Jihar Kano ta yi magana kan zargin kisan kiristoci da barazanar Amurka na Kawo farmaki Najeriya.

Malaman addinin musuluncin sun roƙi ‘yan Najeriya da su kwantar da hankali su kuma mika lamarin ga Allah SWT ta hanyar dagewa da addu’a.

Sheikh Ibrahim Khalil.
Hoton shugaban majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil Hoto: Sheikh Ibrahim Khalil
Source: Facebook

Wace barazana Amurka ta yiwa Najeriya?

Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa ana kashe Kiristoci da gangan a Najeriya, kamar yadda BBC News ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jerin kungiyoyin duniya da suka karyata Trump kan zargin da ya yi wa Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Trump ya kuma bayyana cewa da yiwuwar Amurka ta kai farmaki Najeriya domin dakatar da abin da ya kira “kisan kare dangi da ake yi wa Kiristoci.”

Wannan zargi ya tayar da hankulan mutane tare da haddasa muhawara mai zafi a fadin ƙasar nan.

Malaman Kano sun ba da shawara

Da yake magana a madadin Majalisar malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce wannan lokaci da ake bukatar nutsuwa da haɗin kai, ba firgita ko yada maganganu marasa amfani ba.

Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ne shugaban majalisar malaman addinin musulunci ta Kano, ya ce:

“Majalisar Malamai na kira ga ‘yan Najeriya, Musulmi da Kirista, su tashi tsaye wajen yi wa kasarsu da yan uwansu addu’a game da wannan lamari,” in ji Sheikh Khalil.
“Kowane ɗan Najeriya ya yi addu’a bisa imanin da yake da shi da kuma koyarwar addininsa. Idan Kirista ne, ka roƙi Ubangiji bisa addininka; idan Musulmi ne, ka nemi taimakon Allah cikin addu’a.”

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

Sakon malaman Kano ga musulmai

Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci al’ummar musulmi su dage da addu’o’i daga ranar Asabar zuwa Litinin, da kuma a sauran kwanaki domin Allah Ya kawo saukin lamarin.

“Wannan abu ya shafi kowa, babba da yaro. Haka kuma, kowace Juma’a mu riƙa yawaita yin salati ga Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi),” in ji shi.
Sheikh Ibrahim Khalil.
Hoton shugaban Majalisar Malaman Kano, Sheikh Ibrahim Khalil da na Shugaba Donald Trump Hoto: Sheikh Ibrahim Khalil, @RealDonaldTrump
Source: Facebook

Sheikh Ibrahim Khalil ya kuma ba da shawarar yadda ya kamata a shawo kan barazanar Trump cikin hikima da natsuwa domin kaucewa tashin hankali da rabuwar kai.

Ya ce matukar ana son guje wa rabuwar kai tsakanin yan Najeriya a irin wannan lokaci, wajibi a bar shugabannin addinai da na siyasa su jagoranci shawo kan lamrin.

NSCIA ta karyata zargin kisan kiristoci

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar koli ta harkokin addinin musulunci a Najeriya (NSCIA) ta musanta zargin yi wa kiristoci kisan kare dangi a kasar nan.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Sakataren Janar na NSCIA na kasa, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa ikirarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa ba gaskiya ba ne.

Ya kuma bayyana cewa, hakan wata manufa ce ta siyasa da ake yadawa don ganin an hada fada tsakanin mabiya addinan Islama da Kirista a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262